Yan sanda a Kano sun kama mutum 245 da muggan makamai da kwayoyi

Asalin hoton, KIYAWA FACEBOOK
A wani bangare na yaki da aikata muggan laifuka, rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da kama wasu da take zarginsu da aikata laifuka a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Sama'ila Shu'aibu Dikko ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da rundunar 'yan sandan Kano ta kira a shalkwatarsu da ke unguwar Bompai a ranar Alhamis 16 ga watan Disambar 2021.
Dikko ya ce a samamen da jami'an 'yan sanda karkashin rundunar Puff-Adder, ke kai wa a kwaryar jihar domin kakkabe masu aikata laifi, sun yi nasarar kama mutum 245 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da: Fashi da makami, da satar mutane domin neman kudin fansa, da barayin shanu, da satar motoci, da 'yan daba, da ta'ammali da muggan kwayoyi, da sauransu, kuma tuni aka gurfanar da wasu daga ciki gaban shari'a domin fuskantar hukuncin da ya dace da laifin da suka aikata.

Asalin hoton, KIYAWA FACEBOOK
Kwamishina Dikko ya zayyana jerin adadin wadanda aka kama din kan zarge-zarge daban-daban kamar haka:
- 'Yan fashi da makami 38
- Masu satar mutane 9
- Masu satar kudi ta internet 12
- Barayin shanu 7
- Masu satar motoci 25
- Barayin Adaidaita sahu 12
- Barayin keke 7
- Wadanda ake zargi da dillancin muggan kwayoyi 17
- 'Yan daba 118
Baya ga wadannan mutanen, 'yan sandan sun kuma kubutar da mutum 6 da aka yi garkuwa da su, domin neman kudin fansa. Haka kuma an samu bindiga 35, ciki har da AK47 da SNG da sauransu, sannan an karbe motoci 26, da adaidaita sahu 14 da kekuna 19, da wukake 92, da goruna, da na'ura mai kwakwalwa 4, da wayoyin salula 54, injin janareto 50 da sauransu. A bangaren dilolin muggan kwayoyi, 'yan sandan sun karbe:
- Tabar wiwi moli 303.
- Kwayar taramadol da ta kai kusan naira miliyan 9.
- Da kwayar rafanol takarda 140.
- Kwalabe 150 na maganin tari mai sinadarin Kodin.
- Da sukudai kwalabe 44
- Da shanu 66.

Asalin hoton, KIYAWA FACEBOOK
An yi wannan samame ne daga farkon watan Nuwamba zuwa Disambar 2021, a kuma wurare daban-daban aka kama mutane bayan samun ingantattun bayanan sirri kan maboya da wuraren da bata garin suke fakewa.
Kwamishinan 'yan sanda Dikko, ya yi kira da al'ummar jihar kano da zarar sun ga wani abu da bai gamsar da su ba ko wani mutum su yi gaggawar sanar da ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko kiran lambar su ta gaggawa 08032419754, ko 08123821575, ko 08076091271, da kuma sauke manhajar "NPF Rescue Me" da ake samu a Play Store na wayoyin komai da ruwanka domin bukatar gaggawa.
Jihar Kano dai ta yi kaurin suna a dan tsakanin nan kan kwacen wayoyin salula ko dai a fizge ko kuma 'yan daba su tare masu Babur din adaidaita sahu su karbe, a wasu lokutan ma har suna amfani da makami irin wukake wajen dabawa mutumin da ya yi musu gardamar bada wayar.
Haka kuma ana ganin daba ta sake dawowa jihar, wanda ba wannan ne karon farko da rundunar 'yan sandan jihar Kanon ta kama 'yan daba ba, ko wadanda ke saida muggan makamai kamar Gora da wukake da gariyo da sauransu.











