Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matakan da wasu manyan Najeriya ke so a ɗauka don magance matsalar tsaro
Wani mai faɗa a ji daga cikin dattijan Najeriya kuma ƙwararren dan siyasa a Najeriya Alhaji Salihu Tanko Yakasai, ya ce zanga-zanga ba za ta taba zama mafita ba ga halin da ƙasar ke ciki ba.
Alhaji Yakasai ya fadi hakan ne a wani taron gaggawa da ƴan siyasa da shugabannin addinai suka yi kan matsalar tsaro da kashe-kashen da ake yawan samu a arewacin Najeriyar.
Shugabannin kabilu daban-daban da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam na cikin wadanda suka halarci taron da aka yi a ranar Litinin a Abuja, babban birnin Najeriya.
Taron da wadannan shugabannin suka kira na gaggawa ya ta'allaka ne kacokan kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.
Da kuma tattaunawa kan abubuwan da suke tasowa na barazanar zanga-zanga da ake fama da ita a wasu sassa musamman na arewacin Najeriya, biyo bayan kashe-kashen da ake ta samu a yankin.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce zanga-zanga ba za ta yi ba, "irin wannan taron da muke yi na dattawa da sarakuna da malamai, a nan za a hadu a samar da mafita ko hanyar magance matsalar.
"Ina cikin wadanda suka fara zanga-zanga a Najeriya a 1953, amma ba ta yi maganin komai ba. Kuruciya za ta sa ka yi zanga-zanga amma ba za ta magance matsala ba," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Tuntuɓar sarakunan gargajiya
Alhaji Murtala Aliyu shi ne babban sakataren ƙungiyar tuntuba ta Dattijan Arewa, kallon wannan matsala ya yi ta fuskar noma.
Ya ce matukar ba a dauki matakan gyara ba, Najeriya za ta fada cikin matsanancin fari na abinci nan da dan lokaci kadan.
"A da yadda da ake maganar tsaro a kasar nan shi ne ta fuskar tuntubar sarakuna da hakimai, amma yanzu duk an watsar da su an nuna ba su da amfani.
"Ba yadda za a yi mutumin da ke zaune a ƙauye wanda shi ya sa mutanen wajen ciki da waje a ce maza a yi magana da shi ba.
"Kuma shi kansa rayuwarsa na cikin barazana, ka ga ba zai iya fitowa ya yi magana ba idan shi ma ba shi da kariya.
Ya kara da cewa dole gwamnati ta nemi wadannan mutanen don tatauanwa da su.
"Hatsarin na can gaba idan ba za dauki matakai yanzu ba, don akwai fargabar shiga yanayi na yunwa saboda rashin noma a gonaki," in ji shi.
'Sulhu ne mafita'
Shi kuwa Farfesa Usman Yusuf tsohon shugaban tsarin inshoran lafiya a Najeriya, kuma yana cikin tawagar da ke shiga dazuka domin tattaunawa da ƴan fashin dajin da suka addabi yankin arewacin Najeriya, ya ce akwai bukatar sulhu tsakanin gwamnati da wadannan mutane.
"Jihohi takwas yanzu muka shiga, da Zamfara da Sokoto da Neja da Kaduna da Kebbi da Kwara da Kogi da Katsina.
"Mu ba sojoji ba ne, abin da ya kai mu dazuzzukan don mu ji me ya faru aka kawo ga wannan gaɓa, tun da mu Fulani ne kuma mun san ba haka addini da al'ada suka koya mana ba.
"Su Dogo Gide da Turji da Kacallolin nan duka mun hadu da su. Kuma yawancin matsalolin da suke gaya mana ba komai ba ne sai waɗanda suka fi shafar mutane kai tsaye," in Farfesa Yusuf.
'A cire munafunci a yi magana ta gaskiya'
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'adu Abubakar na uku cewa ya yi gano matsalar da mutum ke fama da ita rabin shawo kann matsalar ne, yanzu rabin matsalar da ke damun Najeriya suke nema.
"Muna son mu ce babu shakka kyakkyawan fatan samun mafita kan matsalolin da ke damun Najeriya, na yi imanin cewa dukkanmu nan mun amince cewa muna cikin matsaloli.
"Kuma ka amince cewa kana cikin matsala to ka samu rabin mafita ga matsalar da kake ciki ne, da irin wadannan tarukan za mu lalubo sauran rabin matsalar da muke fama da ita, mu zauna mu yi magana da juna tsakani da Allah babu munafunci ko san rai.
Abin da ake bukata a shugabanci shi ne ya samar da kyakkyawan yanayi da zai ba ni damar gudanar da rayuwata da addinina yadda ya kamata ba tare da wata fargaba ba."
Hare-haren yan fashin daji da satar mutane domin karbar kudin fansa na daga cikin manyan matsalolin da ‚yan kin arewacin Najeriya ke fama da shi.