Shin dabar siyasa tana neman dawowa ne a jihar Kano?

Harin da wasu matasa suka kai a ofishin siyasa na dan majalisar dattawan Najeriya da ke wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin a birnin Kano, ranar Alhamis, ya kara fito da matsalar daba a siyasar jihar wadda ta fi yawan jama'a a arewacin kasar.

Sanata Jibrin, jigo ne a ɓangaren jam'iyyar APC da ya raba gari da ɓangaren gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Ganau sun shaida wa BBC cewa matasan da suka kai hari ofishin sun fi 100, inda suka kona shi tare da fasa gilasai.

Hakan na faruwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɓangaren Gwamna Ganduje tare da tabbatar da jagorancin ɓangaren tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, wanda yake kawance da Sanata Jibrin suna zargin gwamnatin jihar da nuna musu ''wariya a jam'iyyar APC".

Rikicin siyasar APC a Kano na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya tun bayan gudanar da zaɓen shugabannin jam'iyyar ɓangare biyu, inda wasu ke ganin rabuwar kai a Kano wata babbar ɓaraka ce ga APC a Najeriya baki daya.

Sai dai babban abin da ya fi jan hankali shi ne yadda ake amfani da matasa wajen kai hari ga abokan hamayyar siyasa. Masana harkokin siyasa na fassara hakan a matsayin "dawowar siyasar daba" a jihar.

Sun bayyana cewa amfani da daba wajen cimma manufofi na siyasa ya dade yana faruwa a jihar Kano da ma wasu jihohin kasar, amma lamarin ya yi sauki a shekarun baya saboda karuwar wayewar siyasa da kuma yadda ake fadakar da matasan.

Amma a shekarun baya bayan nan abubuwa da dama sun faru da suka nuna irin tashin hankalin da matasa masu ayyukan daba suka jefa jihar.

Takaddama kan wanda zai gaji gwamna Ganduje a 2023

Kabiru Sai'du Sufi, Malami a Sashen Koyar da Harkokin Siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano ya shaida wa BBC Hausa cewa a wannan Jamhuriya, lamarin ya ''tarbarbare'' ne bayan zaben da bai kammala ba na gwamnan jihar Kano a 2019 wanda aka fi sani da inconclusive. Masanin kimiyar siyasar ya ce ''mun ga yadda aka rika amfani da 'yan daba lokacin wancan zabe kuma ba a dauki wani mataki ba.''

"Wannan ne ya sa aka kara wa wannan dabi'a ta amfani da 'yan daba kaimi domin kuwa duk wanda ya dauki hayarsu yana da yakinin cewa duk abin da suka yi ba za a dauki mataki ba. Baya ga haka akwai kuma batun tunkarar zaben 2023; sannan ga samun baraka a cikin jam'iyyu".

A baya bayan nan dai 'yan siyasa musamman na jam'iyyar ta APC sun rika sukar juna bayan rabuwar da suka yi, sai dai tun kafin hakan an rika jifan juna da muggan kalamai da kuma amfani da 'yan daba domin biyan bukatu na siyasa.

Hakan kuwa ya yi kamari ne bayan da mai dakin gwamnan jihar Kano, Hafsatu Ganduje, ta yi nuni da cewa Kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo ne ya dace ya gaji mjinta a zaben gwamna na 2023.

'Yan siyasa da dama sun fassara kalaman da cewa alama ce ta cewa tuni aka ware 'yan bora da 'yan mowa kuma an rufe kofa ga duk wanda yake neman zama gwamnan jihar ta Kano a karkashin jam'iyyar APC. To amma daga bisani gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba a fahimci kalaman mai dakin gwamnan ba ne.

Tun daga wancan lokaci ne yanayin siyasa ya kara yin zafi tsakanin bangaren Murtala Sule Garo da kuma Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma ake rade-radin yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

Masana harkokin siyasa irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge sun ce kokawar neman iko na cikin abubuwan da suka ta'azzara amfani da 'yan daba wajen cimma buri na siyasa.

Shi ma Malam Kabiru Sufi ya ce dukkan bangarorin suna da hannu wajen amfani da 'yan daba a 'yaki' irin na siyasa.

Ina mafita daga matsalar?

Wasu daga cikin manyan tashe-tashen hankula na daba da aka fuskanta sun hada da fadan Hauwan Daushe tsakanin magoya bayan Sanata Barau Jibrin da na Murtala Sule Garo, da kuma rigima tsakanin dan majalisar dokoki ta tarayya da ke wakiltar Kano Municipal, Sha'aban Sharada da shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Fa'izu Alfindinki inda aka yi zargin an yi amfani da wasu matasa wajen rusa gini da ba a kammala ba na cibiyar horas da matasa wanda Honourable Sharada ke yi. Ko da yake Alhaji Alfindinki ya ce filin da dan majalisar yake ginin a kai kwace shi Honorouble Sha'aban ke so ya yi.

Masanin siyasa Malam Sufi ya ce za a magance wannan matsalar "idan shugabannin addini da na siyasa suka fito fili suka nuna rashin amincewarsu da irin wadannan ayyuka na 'yan daba domin kuwa idan aka ci gaba da samun rikici irin wannan lamarin zai wuce siyasa ya koma kai wa al'umma hare-hare."