Me ya sa ake yawan kai hare-hare gidajen yarin Najeriya?

Harin da wasu 'yan bindiga suka kai gidan yarin Jos, babban birnin jihar Filato da ke arewacin Najeriya inda suka kubutar da fursunoni kusan 300 ya aza alamar tambaya game ingancin tsaron da ke gidajen yarin kasar.

A ranar Lahadi da almuru ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a gidan yarin na Jos, inda suka ci karfin jami'an tsaron da ke ciki kana suka kubutar da fursononi 262, a cewar alkaluman hukumar da ke lura da gidajen yarin kasar.

Hukumomi sun ce fursunoni tara sun mutu yayin da ma'aikacin gidan yarin daya ya rasu, kana aka kashe dan bindiga daya, ko da yake sun kara da cewa an sake kama fursunoni goma da suka tsere.

Wannan lamari dai ya tashi hankalin wasu mazauna jihar musamman ganin cewa gidan yarin yana yankin hukumomin tsaro da dama na kasar suke da hedikwatarsu, ciki har da hedikwatar rundunar 'yan sanda.

Kazalika lamarin na faruwa ne wata daya bayan harin da wasu 'yan bindiga suka gidan yarin Abolongo da ke jihar Oyo inda suka kubutar da fursunoni kusan 575.

Kafin wannan, rahotanni sun nuna cewa an kubutar da fursunoni sama da 2,000 a hare-hare biyu da 'yan bindiga suka kai gidajen yari buyu: ranar 13 ga watan Satumba, an kubutar da fursunoni 240 a Kabba da ke jihar Kogi, yayin da 'yan bindiga suka yi amfani da abubuwan fashewa suka fasa gidan yarin, sai kuma ranar 5 ga watan Afrilu inda aka kubutar da 1,800 a gidan yarin Owerri da ke jihar Imo.

Lokacin da aka kai hari a gidan yarin jihar Oyo, Ministan Harkokin Cikin Gidan Najeriya, Ogbeni Rauf Aregbesola ya ce an yi hakan ne "da zummar kunyata gwamnatin kasar".

Mr Aregbesola ya sha cewa suna daukar matakan kare gidajen yarin daga hare-haren 'yan bindiga, yana mai cewa "Ina mai tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta yi dukkan kokari wajen kama wadanda suka kai hari kan gidajen yarinmu da kuma wadanda suka tsere".

Sai dai da alama wannan alwashi na Minista bai yi tasiri ba domin kuwa ana ci gaba da kai hare-hare kan gidajen yarin.

Hakan na faruwa ne a yayin da kasar take ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren 'yan bindiga da na masu garkuwa da jama'a, kuma masu lura da lamarin tsaro sun ce hare-hare a gidajen yaroin za su ta'azzara wadanna matsaloli.

Wani masanin tsaro, Malam Abdullahi Yelwa, ya shaida wa BBC cewa hare-haren da ake kai wa gidajen yarin wata alama ce da ke nuna cewa "gwamnati ba ta cimma muradun da aka gina su - halayyar su fursunonin ba ta sauya ba."

"Wadannan fursunoni da aka kubutar za su dawo su ma su kubutar da abokansu, wasu kuma daga cikinsu hatsabibai ne da fiddo su zai dagula lissafin jami'an tsaro da tayar da hankulan jama'a".

Masanin tsaron ya kara da cewa hare-haren da ake kai wa gidajen yarin sun nuna sakacin tsaro daga bangaren gwamnati yana mai cewa za a ci gaba da fuskantar irin wadannan hare-hare har sai lokacin da gwamnati ta karfafa tsaro a gidajen yarin.

"Wani abu kuma shi ne cunkoson da ke gidajen yarin kasar nan; gwamnati tana sanya fursunoni ninkin ba ninkin abin da ya kamata su sanya a gidajen yarin. Shi ne ya sa suka cika suka tumbatsa, kuma hakan wata gazawa ce za ke iya haddasa matsalar tsaro," in ji Malam Abdullahi Yelwa.

Masanin ya ce dole gwamnati ta dauki matakan da za su hana kai mutane "gidan yari - irin su inganta rayuwar mutane lamarin da zai hana su aikata laifuka da kara tsaro a gidajen yari."