Ibrahim Shekarau: Rashin iya jagorancin Ganduje ne silar rikicin APC a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kanon Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi zargin cewa rashin iya jagorancin jam'iyya daga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne silar rikicin da jam'iyyar APC ke fama da shi a jihar.

Sanata Shekarau ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da BBC a Kano jim kaɗan bayan kammala wani taron da ya yi da magoya bayansa kan halin da shugabancin jam'iyyar ta APC ke ciki a jihar da kaddamar da kwamitin majalisar shura ta gidan siyasarsa. 

Shekarau ya zargi shugaban Jam'iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas da iƙirarin cewa APC a Kano ta Ganduje ce da mai ɗakinsa Gwaggo da kuma shi kansa Abdullahi Abbas ɗin.

Ya kuma ce an mayar da su saniyar ware a duk wasu al'amura na Kano kama daga batun taron jam'iyya zuwa sauran tarurruka da ba a rasa ba inda ya ce ba a ba su goron gayyata.

"Babu wani taro da aka gaya mini da ban je ba, kuma akwai abin da ake kira elders, me zai hana gwamna ya kira mu ya ce don Allah ina gani idan muka ba wane muna sha'awar ya yi ciyaman, idan da gyara za mu gyara maka, idan da wata illa za mu fada, idan babu illa za mu ce babu damuwa," in ji shekarau.

Tsohon gwamna Shekarau ya ce ƙorafin da suka yi kan rikicin da ke tsakaninsu da ɓangaren Ganduje a yanzu yana gaban kwamitin sasanta rikicin APC na ƙasa wato kwamitin da su Abdullahi Adamu ke jagoranta.

"Majalisar shurar mu tana nan, yau shekara goma, amma shurar nan tana da alaƙa da siyasa abokan shawara ne na siyasa, sun san muna da tsari, gwamnati da ya yi zaɓen ƙananan hukumomi ya ƙare, amma dai zaɓen jam'iyya muna hakki."

Rikicin da ke tsakanin ɓangaren Ganduje da na Shekarau a Kano ya yi sanadin rabuwar jam'iyyar gida biyu inda Ahmadu Haruna Zago jagorantar ɓangaren Shekarau sai kuma Abdullahi Abbas ɓangaren Ganduje.

Tushen rikicin APC a Kano

Tun bayan zaben shugabannin majalisar kananan hukumomi da zabukan shugabannin jam'iyyar APC na gundumomi da kananan hukumomi ake yi wa ƴan tsagin Shekarau, laƙabi da 'ƴan bakwai.

Mutanen sun haɗa da Senata Kabiru Ibrahim Gaya (kodayake daga baya ya fice daga wannan tafiyar) da Senata Barau Jibrin da Hon. Sha'aban Ibrahim Sharada da Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe da wasu suka yi zargin cewa ana mai da su saniyar-ware, saboda ba a tuntuɓar su ballantana ma a ba su wani kaso daga cikin waɗannan muƙaman.

Kenan ana kokarin kwashe musu ƙafa ne a zaben shekara ta 2023. Wannan ne ya sa suka rubuta takardar korafi ga hedikwatar jam'iyyar APC suna sukar yadda zabukan suka gudana tare da jaddada cewa ba za su amince da su ba.

Ƴan magana dai sukan ce abokin kuka ba a boye masa mutuwa. Sannu-sannu, haka wannan gangami na Ƴan bakwai ya ci gaba da tuntubar masu irin nasa ra'ayin har a karshe suka ware suka yi nasu zaben shugabannin jam'iyyar APC na jihar Kano, inda Alhaji Ahamdu Haruna Zago ya zama shugaba.

A bangaren Gwamna Ganduje kuma, Alhaji Abdullahi Abbas aka zaɓa a matsayin shugaba, kuma tuni kowane tsagi ya rantsar da nasa shugaban.

Tsagin Ganduje dai ya ce zaben da ya gudanar shi ne na kwarai saboda kwamitin da hedikwatar jam'iyyar ta tura jihar shi ne ya sa ido a kan zaben.

Amma tsagin Shekarau shi ma yana ikirarin cewa shi ma Ƴan kwamitin hedikwatar jam'iyyar APC ne suka je wurin nasa zaben.