Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rwanda ta soma amfani da babura masu amfani da lataroni
- Marubuci, Daga Gabriella Mulligan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology of business reporter
Didier Ndabahariye ya kwashe shekara 12 yana sana'ar acaba a Kigali - yana daya daga cikin dubban 'yan acaba a birnin.
Kwanakin baya ya sauya babur dinsa zuwa wanda yake amfani da lataroni a babban birnin na Rwanda.
"A lokacin da na fara amfani da wannan babur din ba na jin dadi saboda na saba da wanda yake aiki da fetur.
"Daga bisani na gane yaddda ake aiki da babur mai amfani d lataroni, kuma daga nan ne na soma tara kudi," a cewar Didier.
Yana daya daga cikin mutum 60 da ke amfani da babur mai aiki da lataroni na kamfanin Ampersand da ke Rwanda.
"Yanzu ina son wadannan babura - babur mai amfani da lataroni yana dadewa yana aiki ba tare da wata matsala ba, ba kamar mai amfani da fetur ba - kuma yana da dadin sha'ani, ga laushi."
Kamfanin Ampersand ne ya dauki alhakin kawo wannan sauyi daga Babura masu amfani da fetur zuwa masu amfani da lataroni kuma yana fatan nan da shekara biyar dukkan baburan da Rwanda za su rika aiki da lataroni.
Wannan gagarumin aiki ne - akwai Babura kusan 25,000 a Kigali, wasu daga cikinsu suna irga-zirgar awa 10 a kwana daya, inda suke kwashe tafiyar daruruwan kilomita a kullum.
"Babura su ne kusan rabin abubuwan hawan da ake amfani da su a wannan bangare na duniya," a cewar shugaban Ampersand Josh Whale.
"Injinansu masu sauki bas a fitar da hayaki mai gurbata muhalli kamar yadda ake gani a motocin zamani ko babura a wasu wuraren."
"A Rwanda, masu tukin ababen hawa suna kasha kudi sosai wajen sayen fetur a duk shekara fiye da yadda suke kashewa wajen sayen sabon babur. Mun nuna cewa akwai zabi kamar yadda muka kawo wadannan Babura da ba a kasha musu kudi da yawa, sannan suna amfani da lataroni maras yawa, kuma dawainuyar da ake yi a kansu ba ta da yawa."
Ampersand ya ce kasha kudi kalilan sayen sayen fetur da kuma dawainiyar da ake a kan wannan babur za sus a kudin da matuka baburan ke samu su ninka.
An kiyasta cewa Babura miliyan biyar ne suke yawo a kan titunan kasashen Gabashin Afirka, don haka matakin na Ampersand zai rage yawan iska mai gurbata muhalli da ake fitarwa a yankin.
Ampersand ba kawai harkar fasaha yake yi ba. Yana hada sabban Babura da batur da kuma tasoshin cajin batura.
Kowanne babur yana da sassa a kalla 150, wadanda ake hadawa a Kigali. Abu mafi muhimmanci shi ne yadda injiniyoyin Ampersand suka tsara baturan na musamman a Rwanda. Daga nan za a kera su a kasashen sanna a shigo da su kasar ta Rwanda inda injiniyoyin kasar za su hada su.
A halin da ake ciki Ampersand yana da ma'aikata 73 a kamfanin kera baburansa da ke Rwanda kuma yana Shirin komawa sabon ofis a wannan watan ganin cewa al'amuransa na kere-kere suna bunkasa.
"A halin da ake ciki za mu ci gaba da kasancewa a matsayin kamfnin Babura, da sassansu da kuma gyaransu. Sai dai za mu so yin aiki da manyan kamfanonin da ke yin babura masu amfani da fetur domin ganin yadda za su rungumi tsarinmu."
"Har yanzu ba mu yi karfi ba amma muna so mu yi aiki cikin hanzari - kamar yadda yanayi yake bukata - sannan mu yi abubuwa masu wahala da sauri. Za mu yi farin cikin hada gwiwa da wasu kamfanonin domin cimma burinmu," in ji Mr Whale.
Kamfanin ya kafa cibiyoyin sauya batura - inda matuka za su je da tsofaffin batiransu a yi musu caji - inda suke da cibiyoyi biyar a birnin Kigali.
An kashe kusan $5,000 (£3,700) wajen kafa kowacce cibiya - kuma kamanin ya ce zai iya kafa cibiyoyi kusan wadanda kudinsu bai wuce na gidan man sayar da fetur daya ba.
Gwamnatin Rwanda tana da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen ganin an samu sauyi daga harkar sufuri mai amfani da fetur zuwa mai amfani da lataroni.
Za ta yi asarar harajin man fetur - amma moriyar da za ta ci za ta hada da rage shigar da fetur kasar da samar da ayyukan yi.
Gwamnatin Rwanda tana bayar da tukuici ga wadanda suka rungumi baburan da ke amfani da lataroni.
Hakan ya da rage wa masu amfani da babur din kudin cajinsa da ba su wurin fakin mai kyau da sauransu a birnin Kigali.
A Rwanda, tun shekarar 2019 kamfanin Volkswagen yake hada gwiwa da Siemens wajen samar da ababen hawa masu amfani da latarori, lamarin da ya kai ga samun motoci 20 kirar Golf masu aiki da lataroni da tasoshin cajinsu biyu a Kigali.
Ampersand yana ganin kaddamar da ababen hawa masu aiki da lataroni a Rwanda matakin farko ne ga kasashen Afirka na rungumar wannan hanya, inda yanzu haka kamfanin yake kaddamar da ababen hawa masu aiki da lataroni a Kenya da ke makwabtaka, kuma nan gaba zai je wasu kasashen.