Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Riga-kafin kansar mahaifa na rage kamuwa da cutar da kaso 90 cikin 100
- Marubuci, Daga James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
Allurar riga-kafin cutar kansar mahaifa da ake kira Human Papillomavirus ko HRV ta rage yawan masu kamuwa da cutar da kusan kashi 90 cikin 100 kamar yadda bayanai na ainihi na farko suka nuna.
Cibiyar bincike a kan cutar kansa da ke Birtaniya ta bayyana binciken a matsayin "gagarumar nasara''. Kuma ya nuna cewa maganin yana ceton rayuka.
Kusan duk cutar kansar mahaifa, kwayoyin cuta ne ke haifar da su, kuma fatan da ake yi shi ne allurar riga-kafin za ta iya kawar da cutar.
Masu binciken sun ce nasarar na nufin wadanda aka yi wa allurar riga-kafi watakila ba za su yi gwajin cutar kansar mahaifa da ake kira Smear ba kamar yadda aka saba yi .
Ana ba wa 'yan mata allurar tsakanin shekaru 11 zuwa 13, ko da yake ya danganta da inda suke zaune a Burtaniya.
An kuma bayar da rigakafin ga yara maza tun shekarar 2019.
Binciken da aka wallafa a mujallar Lancet, ya yi nazari kan abin da ya faru bayan da aka samar da riga-kafin ga 'yan mata a Ingila a shekarar 2008.
Wadannan dalibai yanzu sun kai shekaru 20. Binciken ya nuna raguwar kwayoyin halitta da ke karuwa a jikin mutum wadanda idan ba a duba ba za su iya kawo cutar kansa da kuma raguwar cutar sankarar mahaifa da kashi 87 cikin 100.
"Allurar ta yi tasiri sosai ," in ji Farfesa Peter Sasieni, daya daga cikin masu bincike a kwalejin King's ta birnin Landan.
Sai dai raguwar da aka samu kan matasan da aka yi wa allurar ba ta kai kamar ta masu shekara 11 zuwa 13 ba.
Wannan nada nasaba da matasa kalilan da suka gabatar da kansu domin a yi musu allurar kuma ana bukatar a yi mu su allurar kafin su fara jima'i.
Gaba daya binciken ya yi kiyasin allurar riga-kafin cutar kansar mahaifa ta hana mutum kusan 450 kamuwa da cutar kansa da mutum fiye da dubu 17 samun kwayoyin hallita da karuwa a jikin mutum da ake kira pre-cancers.
Farfesa Sasieni ya ce wannan "somin tabi ne" saboda wadanda aka yi wa allurar har yanzu matasa ne wanda wani abu ne mai wuya su kamu da cutar, don haka alkaluman za su karu nan gaba.
Gwaji
A halin yanzu, ana so mata su yi gwajin cutar kansar mahaifa bayan shekara uku zuwa biyar.
Sai dai Farfesa Sasieni ya ce ''tabbas ''ana bukatar sake tunani bayanan wannan sakamako.
Ya fada min : "Ya kamata ya zaman abin da zai sa masu tsara manufofi su farga, mata za su karanta wannan kuma za su fahimci "me ya sa zan je a yi man gwaji?''.
"Ina fata za mu dawo da wani sabon shirin gwaji, sau biyu zuwa uku a rayuwarmu kuma a ci gaba da yi wa matan da ba a yi musu allurar ba gwaji ."
Wannan ba shi ne ƙarshen magana akan allurar HPV ba. Har yanzu akwai tambayoyi game da tsawon lokacin da kariyar ke daɗewa da kuma ko akwai buƙatar sake yin allurar bayan wani lokaci.
Akwai nau'ikan kwayar cutar sankarar mahaifa sama da dari.
Birtaniya ta soma amfani da maganin da ke ba da kariya daga biyu daga cikinsu kuma ta na shirin gabatar wani da ke ba da kariya daga kwayoyin cuta tara, ciki har da manya abubuwan da ke janyo kuraje a al'aurar mutane da ake kira "warts."
Nau'ikan kwayar kansar mahaifa sun sauya kwayoyin halitta na DNA da ke haifar da cutar kansar ta mahaifa.
Kwayoyin cutar na bazuwa ne ta hanyar jima'i ta farji da ba ka da dubura, azzakari da wasu ciwon sankara na kai da wuya.
Sai dai kashi 99 cikin 100 na cutar kansar mahaifa, kwayoyin cutar Papillomairus ne ke haifar da su.
Wannan shi ne dalilin da ya sa kasashe fiye da 100 suka fara amfani da allurar riga-kafin a matsayin wani bangare na shirin Hukumar Lafiya ta Duniya na gab da kawar da cutar kasar mahaifa.
Dokta Vanessa Saliba, wadda kwarariyar likata ce a fanin binciken cututtuka a wata cibiyar kiwon lafiya da ke Burtaniya ta ce sakamakon binciken ya kasance ''na ban mamaki'' kuma ya nuna cewa maganin na "ceto rayukan mutane ta hanyar matukar rage yawan matan da ke kamuwa da cutar kansar mahaifa" .
Shugabar cibiyar bincike kan cutar kansa a Burtaniya Michelle Mitchell ta ce: "wannan rana ce mai cike da tarihi ganin binciken farko ya nuna cewa riga allurar rigakafin HPV yana kuma zai ci gaba da kariya ga dubban mata daga kamuwa da cutar kansar mahaifa."