Yadda tarihin China ke tasiri kan tunanin Shugaba Xi Jinping

Karuwar tsamin dangantaka tsakanin Taiwan da China ta sa wasu sun fara tunanin yadda Shugaba Xi Jinping ke kallon kasarsa.

Sai dai abubuwan da suka faru a baya za su yi karin haske kan haka, a cewar Rana Mitter, malamin tarihi a Jami'ar Oxford da ke Birtaniya.

China ta zama daya daga cikin manyan kasashe mafi karfin fada a ji a duniya, abin da ba a ko hasashe a da.

A wasu lokutan karfin China na karuwa ne saboda kokarin kulla hulda da kasashen duniya, kamar yadda ta rattaba hannu a yarjejeniyar magance matsalar sauyin yanayi ta Paris.

Haka kuma sai an yi da kyar za a iya ja da China, irin yadda ta kafu wurin kulla huldodin kasuwanci a sama da kasashe 60 a duniya musamman wadanda kasashen turai suka hana a bashi.

Gwamnati a Beijing ta kuma yi tur da Amurka kan huldar da ta kulla da kasashen Australiya da Birtaniya ta AUKUS.

Kazalika ta gargadi Birtaniya cewa ta saurari abin da zai biyo baya kan amincewa da bai wa 'yan Hong Kong damar zama 'yan kasar.

Bugu da kari ta sanar da Taiwan cewa ta shirya zama wani bangare na China.

Xi Jinping ne Shugaban China da ya daga sunanta a matsayin mai karfin fada a ji tun bayan Mao Zedong wanda ya yi mulki zamanin cacar baka.

Ba a taba samun wanda ya fito da ita ba a matsayin kasa mai karfin fada a ji kamar Mr Xi.

Ra'ayin gargajiya

Sama da shekaru 2000 al'ummar China na da ra'ayin gargajya na 'Confucian', wanda ke bai wa al'umma kwarin gwuiwar cewa shugabanni za su kula da na kasa da su.

Al'ummar China sun yi amanna da hakan har zuwa lokacin juyin juya hali a 1911, a lokacin da aka kifar da gwamnatin karshe da ke tafiya kan tsarin confucism.

A lokacin ne kuma tsarin kwamusanci ya samu gindin zama a China.

Daya daga cikin masu wannan tsari na kwamusanci shi ne Mao Zedong, wanda ke adawa sosai da tsohon tsarin da 'yan kasar suka saba da shi a lokacin da ya yi mulki daga 1949-1976.

Daga baya kuma an samu masu adawa da tsarin confucism da suka rungumi wani bangare nashi.

Hatta Shugaba Xi Jinping ya aminta da wani bangare na tsarin, har ma ya taba kai ziyara mahaifar al'adar a Qufu.

Shekara da shekaru cikin wulakanci

Tarihi ya nuna cewa rikice-rikicen da suka faru a karni na 19 da na 20 sun yi tasiri sosai kan yadda China ke kallon duniya.

A lokacin yake-yaken Opium da aka yi a tsakiyar karni na 19 tarihi ya nuna yadda kasashen Yamma suka yi amfani da karfi a kan China.

Kuma a tsakanin shekarun 1840 zuwa 1940 lokaci ne da aka yi wa lakabi da 'karnin wulakanci'.

A wannan karni ne duniya ta shedi gazawar China a fada da kasashen Turai da kuma Japan.

A lokacin ne China ta rasa zabi da ya sa ta bar wa Birtnaiya iko da Hong Kong, ta saki yankin Munchuria da ke arewa maso gabashin kasar ga Japan, yayin da kasashen Turai kuma suka kwace mata damarmakin kasuwanci da ta ke da su a duniya.

Hakan ya haddasa rashin yadda da 'yan China ke da ita kan manufofin sauran kasashen duniya a kanta. Hakan ya kuma sa China ta rika taka tsantsan da wasu lamurran kasasshen duniya, kamar ficewarta daga kungiyar cinakayya ta duniya wato WTO.

China ta rika kallon cewa wasu kasashen waje ne ke jan ragamar kasuwancinta, wani abu da jam'iyar kwamusanci ta sha alwashin dakilewa.

Kawar da aka manta da ita

Sai dai kuma a wasu lokutan wasu abubuwa marasa dadi kan haifar da abin da ake fata daga baya.

China ta shedi hakan a lokacin yakin duniya na biyu bayan arangamar ta da Japan a 1937.

Sannan daga baya lokacin da kasashen Yamma da take kawance da su suka taya ta yakin nahiyar Asiya na Pearl Harbour a 1941.

A lokacin wadannan yake yake China ta rasa sama da mutun miliyan 10 inda ita kuma ta kama sojojin Japan 500,000 wanda har yanzu yana nan rubuce ana karantawa a litattafai da fina-finai.

A yau China na bayyana kanta a matsayin mai yaki da mulkin kama karya da karfa-karfa, kuma tana gefe daya da Amurka da Burtaniya da Rasha.

China na yiwa kanta kallon jagora ko kuma sarauniyar kasashe masu tasowa, wani mataki da tsohon shugaba Mao ya dora ta akai.

Tarihin wannan zamani na tasiri kan yadda jam'iyyar komusanci ke tafiyar da shugabanci.

Sai dai akwai wasu abubuwa da ake saurin mantawa da su, kamar yunwa da matsin tattalin arziki ya haifar daga 1958 zuwa 1962 wanda a yanzu ba a ambaton a China.

Ana kuma amfani da wasu yake-yake da aka yi a wannan zamani don takalo wasu sabbin rigingimu.

Alal misali tsamin dangantaka tsakanin Amurka da China ya sa an rika yin fina-finai da ke tunawa da yankin Koriya da aka yi daga 1950 zuwa 1953, wanda China suka sauya wa suna zuwa "yakin bijirewa Amurka."

Markisanci

Haka kuma tsarin tafiyar da Marxism ya yi tasiri a siyasar China, ana kuma ganin shaidar hakan a karkashin mulkin Shugaba Xi mai ci.

A ilahirin karni na 20, Mao Zedong da wasu manyan 'yan siyasa a jam'iyyar kwamusanci sun ja da tsarin Marxism.

Mulkin Shugaba Xi ne ya kara bayyana nasabar takun sakar da ke tsakanin Amurka da China da ra'ayin Marxism.

Taiwan

Gwamnati a Beijiing ba ta taba matsawa daga matsayinta ba na ayyana tsibirin Taiwan a wani bangaren China.

Kuma dama tun asali tarihin Taiwan ya nuna cewa tsibirn na tsakiyar ja-in-jar siyasar China.

A shekarar 1895 lokacin da Japan ta ci ta da yaki, an tilasta wa China mika Taiwan ga Japan din na tsawon rabin karni.

Daga baya kuma aka hade ta da China daga shekarun 1945 zuwa 1949.

A karkashin mulkin Mao China ta gaza mamae Taiwan, har sai bayan da China ta rika wa Koriya ta Arewa ta yaki Koriya ta Kudu a shekarar 1950.

To amma yakin na Koriya ya sa Taiwan ta zamo wani tsibiri da ya haddasa yakin cacar baka.

Daga baya kuma aka hade ta da China daga shekarun 1945 zuwa 1949.

A karkashin mulkin Mao China ta gaza mamae Taiwan, har sai bayan da China ta rika wa Koriya ta Arewa ta yaki Koriya ta Kudu a shekarar 1950.

To amma yakin na Koriya ya sa Taiwan ta zamo wani tsibiri da ya haddasa yakin cacar baka.

Mao ya kai wa Taiwan hare hare a shekarar 1958, amma bayan shekaru 20 ya yi watsi da yankin.

Kuma duk da gayara dangantaka tsakanin China da Amurka a 1979 ba a warware makomar Taiwan ba.

Shekaru 40 bayana haka Shugaba Xi Jinping na ci gaba daga inda sauran shugabanni suka tsaya, na bayyana China a matsayin wadda ke da wuka da nama kan makomar Taiwan da Hong Kong.

Sai dai kuma babu abin da hakan ke haifarwa ban da karuwar kiyayyar China a zukatan al'ummomin Taiwan da Hong Kong.

Farfesa Rana Mitter yana koyarwa a Jami'ar Oxford inda ta goge a fannin tarihi da siyara China ta zamani Ya rubuta littafi mai suna China's Good War: How World War II Is Shaping a New Nationalism