Ba gudu ba ja da baya kan shugabancin Zago na APC a Kano - Shekarau

Asalin hoton, Ibrahim Shekarau Facebook
Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau ya kafe cewa Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam'iyyar APC zababbe na jihar Kano.
Tsohon gwamnan na Kano ya jaddada wannan matsayi nasa ne a wata sanarwa da ya fitar, sakamakon rabuwar kai da aka samu a zaben shugabannin jam'iyyar da ka yi a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba, 2021, inda aka yi zabe bangare biyu, wanda kuma har kawo yanzu uwar jam'iyyar ta kasa ba ta fitar da wata tartibiyar sanarwa kan shugabancin da ta amince da shi ba.
A yayin zaben na Asabar, bangaren gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zabi tsohon shugaban jam'iyyar wanda kuma har lokacin zaben yake matsayin shugaban riko, a matsayin sabon shugaban jam'iyyar, yayin da bangaren Ibrahim Shekaru ya zabi Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban.
Sai dai kamar yadda muka ruwaito muku a baya, shugaban kwamitin da uwar jam'iyyar ta APC ta kasa ta tura jihar ta Kano domin gudanar da zaben Barista Auwalu Abdullahi, wanda ya jagoranci gudanar da zaben na bangaren gwamna a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata, ya bayyana cewa Abdullahi Abbas ne ya yi nasara da kuri'u 3,122.
Babban jami'in ya ce wannan ne ya bai wa Abdullahi Abbas din damar zama sabon shugaban jam'iyyar APC na jihar ta Kano.
Bayan zaben na Asabar an ruwaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cewa sakamakon zaben babbar nasara ce ga jihar Kano, kuma sun san cewa a nan ne uwar jam'iyya ta aika wakilai har guda bakwai wadanda a kan idonsu komai ya gudana kuma sun tabbatar an yi zaben cikin gaskiya da adalci.
Gwamnan ya kara da cewa babu wasu jami'ai da aka tura wani wurin zabe na daban da aka yi, don haka nasu ne halattacce.
Sai dai daya bangaren wanda ke rikici da bangaren gwamnan na Kano, karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau din suma sun gudanar da nasu zaben a yankin Janguza da ke karamar hukumar Tofa a jihar ta Kano, inda suka zabi Alhaji Ahmad Haruna Zago a matsayin nasu shugaban jam'iyyar.

Asalin hoton, NIGERIAPOLICE
Da farko dai sun shirya gudanar da zaben nasu ne a cibiyar koyar da matasa sana'o'i ta Sani Abacha da ke kan hanyar zuwa Madobi, amma kafin su isa an tura jami'an 'yan sanda sun mamaye wurin.
Wannan ya sa suka tafi yankin na Janguza inda suka gudanar da zaben tare da bayyana Ahmad Haruna Zango a matsayin zababben shugaban jam'iyyar APC din a Kano.
Honarabul Tijjani Abdulkadir Jobe, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa da Tofa, wanda yake bangaren na Shekarau, da kuma yana daga cikin wadanda suka shirya zaben na wannan bangare ya ce bangrensu shi ne zaben da uwar jam'iyyarsu ta APC ta yarda da shi.
"Akwai jami'an gabatar da zabe sun je daya wurin sun kuma je inda muka yi zabe idan ba mu saurari jam'iyya ba ai hakan ba za a amince ba.
"Don haka zaben da muka yi shi ne halattace, mu ne a kan tsari, su ba shugabanni ba ne, ba su da wata dama da za su ce sun gudanar da zabe," inji shi.
A waccan sanarwar da Mallam Ibrahim Shekarau ya fitar kan jaddada matsayinsu na cewa Haruna Zago ne shugaban jam'iyyar a Kano, ya tunatar cewa ya jagoranci wasu daga cikin wadanda aka zabe su, daga majalisar kasa, inda ya ce sun shigar da kuka ga uwar jam'iyya a kan rashin gudanar da abubuwan da suka shafi jam'iyyar tare da su.
Ya ce, "Mu zababbu ne, jama'armu suna da hakki. An karbi korafinmu da mutumtawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware takaddamar cikin lumana."
Ya kara da cewa, ''Ina sanar da duk jama'armu, ina cikin jam'iyyar APC daram-dam, za mu tsaya har illa masha Allahu.
"A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulakanci. Mun yi hakuri amma ba za mu lamunci sakarci ba. Korafinmu yana gaban mahukunta. Ba za mu saurari kowa ba sai wadanda muka kai musu kuka."

Waiwaye

Idan bai ba a manta ba a ranar Talata 12 ga watan Oktoba, 2021 ne wasu ƙusoshin jam'iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha'aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam'iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam'iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.
Ko da yake daga baya Santa kabiru Ibrahim Gaya ya nesanta kansa daga wannan magana, inda ya ce shi kam yana tare da Gwamna Ganduje.
Rikicin zaben sabbin shugabnnin na jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriya ba a jihar Kano kawai ya tsaya ba har ma da wasu jihohi na kasar irin su Oyo da Ogun da Abia.

Matakin jam'iyya daga tarayya
Sai dai a wata sanarwa da Sakatare na kasa na kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar a tarayya, Sanata James Akpanudoedehe, ya sanya wa hannu, ya ce zababbun da cikakkun kwamitocin shirya zabuka na jihohi suka jagoranci zabensu ne kawai jam'iyyar za ta amince da su a matsayin wadanda za su jagoranci jam'iyyar na tsawon wasu shekara hudu.
A sanarwar jam'iyyar ta ma musanta wasu zabuka na wasu bangarori da aka bayar da rahotannin an yi, tana cewa 'taron bikin suna ne kawai.'
Sanarwar ta Sanata Akpanudoedehe, ta ma yi barazanar daukar matakan ladabatarwa a kan duk wani dan jam'iyyar da ta ce yana yi mata zagon kasa.
Ta ce jam'iyyar ta samar da kwamitocin gabatar da korafi da kara a kan duk wani zabe, ga wadanda suke da wani koke.












