Matar marigayi Sheikh Abubakar Gumi ta rasu

Matar Shiekh gumi

Asalin hoton, Gumi Family

Allah Ya yi wa ɗaya daga cikin matan marigayi Sheikh Abubakar Gumi Hajiya Aminatu Bintu rasuwa.

Ta rasu ne a ranar Asabar a asibitin 44 da ke garin Kaduna, kamar yadda iyalan Sheikh Abubakar Gumi suka sanar.

An yi jana'izarta bayan La'asar kuma an binne ta inda aka binne mijinta Sheikh Abubakar Gumi, kamar yadda aka bayyana a wani shafin Sheikh Ahmad Gumi.

Ta rasu ne tana da shekara 86 a duniya. Ta rasu ta bar ƴaƴa takwas, maza huɗu mata huɗu

Hajiya Aminatu Bintu ita ce mahaifyar Dr Hamza da kuma Birgediya Janar Abulkadir Gumi

Sauran ƴaƴanta sun haɗa da:

  • Malam Hassan Abubakar Gumi
  • Malam Yusuf Abubakar Gumi da
  • Hajiya Ummulkhair Abubakar Gumi
  • Hajiya Aisha Abubakar Gumi
  • Hajiya Hauwa Abubakar Gumi
  • Hajiya Baraka Abubakar Gumi

Mijinta Sheikh Abubakar Gumi babban malami ne a Najeriya, ɗaya daga cikin waɗanda suka asassa ƙungiyar Izala da ke ɗa'awar tabbatar da Sunnah.

Sheikh Abubakar Gumi shi ne babban Grand Khadi na arewacin Najeriya bayan samun ƴancin kan ƙasar, kuma makusanci ga Firimiyan Arewa Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello.