Thomas Sankara: An fara shari'a kan kisan Che Guevara na Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Jewel Kiriungi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Ouagadougou
Shekara 34 bayan kisan da ya kaɗa mutane na tsohon shugaban ƙasar Burkina Faso a lokacin, Thomas Sankara, mutum 14 na fuskantar shari'a, waɗanda ake zargin su da hannu a kisan mutumin da aka fi sani da Che Guevaran Afirka.
Sojoji ne suka harbe shugaban mai matuƙar kwarjini a lokacin da yake da shekara 37, yayin wani juyin mulki ranar 15 ga Oktoban 1987, lamarin da ya sa babban abokinsa Blaise Compaoré ya maye gurbinsa.
Shekara huɗu kafin nan, Compaoré ne ya tsara gudanar da lamarin da ya zama silar zaman Sankara shugaban ƙasa.
Mista Compaoré na daga cikin mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan amma a yanzu haka yana samun mafaka a ƙasar Ivory Coast mai maƙwabtaka, inda ya tsere bayan tursasa shi ya yi murabus lokacin wata gagarumar zanga-zanga da aka yi ta yi a shekarar 2014.
Ya sha yin watsi da hannu a kisan Sankara kuma ya yi ta gujewa zaman sauraron ƙarar.
Duk da shuɗewar lokaci, Sankara ya ci gaba da zama abin girmamawa a faɗin Afirka - ana yawan liƙa hotunansa a jikin motcin tasi-tasi a faɗin Afirka Ta Yamma, yayin da a Afirka Ta Kudu kuma, babban ɗan hamayya Julius Malema ke bayyana shi a matsayin abin koyinsa.
Me ya sa ake yi wa Sankara kallon gwarzo?
"Muna kallon Sankara a matsayin mai kishin ƙasa. Ya ƙaunaci mutanensa. Ya so Afirka. Ya sadaukar da rayuwarsa saboda mu," a cewar Luc Dimaba, sakatare janar na Kwamitin Tunawa da Thomas Sankara.
A ƙarƙashin mulkinsa ne aka sauya wa ƙasar suna - daga Upper Volta zuwa Burkina Faso, wato ma'ana "Ƙasar Mutane Masu Gaskiya".
Sankara ya yi rayuwar tsantseni. Ya rage yawan albashinsa da na sauran ma'aikatan gwamnati. Ya kuma haramta amfani da direbobin gwamnati da sayen tikitin babbar kujerar jirgi.
Ilimi shi ne babban abin da aka bai wa muhimmanci - a lokacin da yake kan mulki, yawan masu ilimi ya ƙaru daga kashi 13 cikin 100 a shekarar 1983 zuwa kashi 73 cikin 100 a 1987, ya kuma jagoranci gagarumin wayar da kai kan riga-kafi a ƙasar.
Sannan ya ƙwace gonaki daga hamshaƙan masu kuɗi ya miƙa wa manoma talakawa, abin da ya jawo bunƙasa a fannin sarrafa alkama.

Asalin hoton, AFP
Sankara ya yi kira ga haɗin kan Afirka don nuna adawa da abin da ya kira sabon mulkin mallaka na hukumomi kamar su Asusun Lamuni Na Duniya da Bankin Duniya.
An taɓa ambato shi yana cewa: "Duk wanda ya ciyar da kai, zai juya akalarka."
Ya ari wani tsarin manufofin ƙasashen waje da ke ƙalubalantar mamayar Faransa, da ya samu ƙarfin faɗa a ji a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Afirka, kamar su Burkina Faso. Matarsa Mariam ta zargi Faransa da kitsa kisansa.
"Har gobe shi ne shugaban ƙasata. Abin da ya yi wa matasa ya ba mu ƙwarin gwiwa na yin koyi da shi," kamar yadda wani ɗalibin Jami'ar Thomas Sankara a Ouagadougou ya shaida wa BBC.
A shekarar 2019 aka ƙaddamar da wani mutum-mutumi na tagulla mai tsawon mita shida a Dandalin Tunawa da Thomas Sankara da ke tsakiyar babban birnin ƙasar Ouagadougou, sannan a 2020 aka sake gyara shi bayan samun ƙorafe-ƙorafe a kan na farkon.

Asalin hoton, AFP
Mr Damiba ya ce ana shirin faɗaɗa dandalin, da ya haɗa da gina wata babbar hasumaya da za a dinga ganinta daga ko ina a fadin Ouagadougou.
Sannan za a gina wa Sankara wani hubbare, da sinima da laburare duk da sunansa. Ana sa ran waɗannan gine-gine za su aike da saƙonnin muradin juyin-juya halin Sankara ga al'umma ta gaba.
Masu sukarsa fa?
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun sha sukar tsare-tsaren Sankara na neman kawo sauyi.
Wani rahoto da ƙungiyar kare hakkin ɗan adam Amnesty International ta sake a shekarar 1986 ya bankaɗo cewa an kama ƴan hamayyar siyasa aka tsare su ba tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya ba sannan aka azabtar da su.

Asalin hoton, AFP
Serge Theophile Balima wanda ya riƙe muƙamin Minsitan Yaɗa Labarai a mulkin Sankara ya ce: "Ina gaya dinga yin tafiyar hawainiya wajen yarda da batun dimokraɗiyya mai jam'iyyu da dama kuma masu hamayya da shi ba sa iya yi masa magana kuma ba a sauraronsu."
Me ya sa ake ta jan shari'ar?
Ɗan uwansa, Paul Sankara ya ce: "Mun daɗe muna jira, duk tsawon shekara 27 na mulkin Blaise Compaoré. A lokacin mulkinsa ba mu ma taɓa ko da mafarkin yiwuwar yin shari'a ba."

Asalin hoton, AFP
Matarsa ta shigar da ƙorafi a 1997 kan kisan mijinta, amma an shafe shekara 15 kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da bincike.
Kazalika, ba a samu wani ci gaba sosai ba har sai bayan kifar da gwamnatin Mr Compaoré a 2014.
Shekarar da ta biyo baya an gudanar da gwajin ƙwayoyin halitta na DNA a wata gawa da aka tono wacce aka yi zaton tasa ce, amma bayanan gwajin ba su iya tabbatar da hakan ba.
A 2016, hukumomin Burkina Faso sun nemi gwamnatin Faransa da ta saki bayanan soji kan kisan Sankara.
An karkasa waɗannan bayanan aka dinga aika su Burkina Faso bi da bi - na ƙarshen shi ne wanda aka aika a watan Afrilun 2021.
Su waye sauran waɗanda ake tuhuma?
Ana sa ran za a tuhumi tsohon shugaban ma'aikatan Mr Compaoré Gilbert Diendéré da wasu mutum 11 a kotun soji. Suna fuskantar tuhuma "kan kai hari kan tsaron ƙasa", da "kitsa kisan kai" da ɓoye gawarwaki.
Tuni aka kai Diendéré gidan yari, bayan yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 20 kan rawar da ya taka a juyin mulkin 2015 da bai yi nasara ba.

Asalin hoton, AFP
Daga cikin waɗanda ake zargi har da Diébré Jean Christophe, likitan da ya sanya hannu kan takardar tabbatar da mutuwar, inda ya ce tsohon shugaban ƙasar ya yi mutuwar Allah da Annabi ne ba kashe shi aka yi ba. Ana tuhumarsa da sauya bayanai.
Daya mutumin da ake tuhuma Hyacinthe Kafando ba ya nan, kuma shi ne tsohon babban mai tsaron Mr Compaoré, wanda aka saka cigiyarsa a ƙasashen duniya da ba da umarnin kamo shi. Ana zargin sa da jagorantar tawagar da ta kashe Sankara da wasu mutum 12 ɗin.
Wane tasiri shari'ar za ta yi?
Akwai fargabar cewa shari'ar za ta taɓarɓarar da yanayi da dama Burkina Faso ke ciki, wacce ke fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da ƙungiyoyin al-Qaeda da Islamic State.
Har yanzu Mr Compaoré yana da ƙima a ƙasar kuma wasu masu sharhi na gargaɗin cewa wasu sojojin da har yanzu suke mara masa baya ka iya jawo matsala.
Amma babu wasu manyan alamu na hakan.
A hannu guda kuma, Shugaba Roch Marc Kaboré na fatan shari'ar za ta kwantar da hankula da kuma inganta sasantawa a ƙasar.











