Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aryan Khan: An kama ɗan Shah Rukh Khan da miyagun ƙwayoyi
Da safiyar Lahadi ne dai aka cafke babban ɗan tauraron fina-finan India na Bollywood Shah Rukh Khan wato Aryan Khan, mai shekaru 23, kan zargin shan miyagun ƙwayoyi saboda nishadi lokacin wata liyafa.
Ana dai tsare da Khan har ya zuwa 7 ga watan Oktoba kuma babu alamar bada belinsa.
Haka zalika an kuma kama Ashish Mishra, ɗan karamin ministan harkokin cikin gida wanda ake zargi da umartar direbansa ya bi ta kan taron wasu manoma da ke gudanar da zanga-zanga, wanda ya haddasa mutuwa da jikkata mutane.
A cikin 'yan kwanakin nan dai hankulan 'yan kasar ta Indiya sun karkata kan sanin abubuwan da ake ciki game da 'ya'yan sanannun mutanen biyu.
Mutanen biyu Khan na Mishra sun musanta zarge-zargen da ake yi musu, sun ce basu da alaƙa da aikata laifukan biyu.
Amma kuma yanayin yadda jami'an tsaro suka dauki lamarin matasan biyu, da kuma yadda kafafen yada labarai suka fi mayar da hankali kan batun ɗan fitaccen jarumin Shah Rukh Khan, na diga ayar tambaya game da manufar wasu kafafen yaɗa labaran da kuma zargin su da kokarin ''bata sunan masana'antar shirya fina-finai ta Bollywood''
Bankaɗo batun miyagun ƙwayoyin'
An cafke Aryan Khan ne a yayin da ya ke cikin jirgin ruwa mai tsananin gudu da ke tahowa daga birnin Mumbai - inda shi da danginsa ke da zama - a kan hanyarsa ta zuwa Goa, wani fitaccen gari mai jan hankulan masu yawon buɗe ido.
Hukumar sa ido kan masu ta'ammali da miyagun kwayoyi ta kasar (NCB), wacce ta cafke shi tare da wasu da dama, ta ce an tsare su ne a karkashin ''doka mai alaƙa da sha da kuma sayar da miyagun kwayoyi''.
Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa, a bisa la'akari da takardun cafke Khan yawan adadin kwayoyin da aka same shi da su, ba su kai wani kwakkwaran dalilin za zai sa a tsare shi ba.
Lauya mai kare shi Satish Manshinde ya musanta zarge-zargen da babbar murya.
Lokacin sauraron bayanai kan belinsa a ranar Lahadi, ya shaida wa alkalan kotun majistare cewa Khan ''har sau biyu aka yi masa binciken kwakwaf lokacin da yake cikin jirgin ruwan'' kuma ya ce '' babu wasu haramtattun kayayyaki a tare da shi'' kana kuma '' babu wata shaida da ta nuna cewa ya sha wasu miyagun ƙwayoyi.''
Zanga-zanga da tsananin gudun mota da rasa rayuka
Batu na biyu kuma ya danganci Ashish Mishra, ɗan ministan Firaminista Narendra Modi kan harkokin cikin gida Ajay Mishra, ya faru ne lokacin da wata mota daga cikin kwambar motoci a gundumar Lakhimpur ta jihar Uttar Pradesh ta yi bi ta cikin taron manoma masu zanga-zanga.
Gabaki daya, mutane takwas ne suka hallaka a afkuwar lamarin.
Amma kuma kungiyoyin manoma sun ce masu zanga-zanga biyu ne suka hallaka a lokacin da mota ta bi ta kan su, yayinda aka garazaya da sauran mutane biyu suka jikkata zuwa asibiti, kana gungun masu zanga-zangar sun lakada wa ma'aikatan jam'iyar BJP uku da direbansu dukan kawo wuka har sai da suka mutu.
Rahotannin farko sun nuna cewa Ashish Mishra na kokarin tserewa gudun kada masu zanga-zangar su lakada masa duka.
Daga bisani kuma ya bayyana cewa ba ya cikin motar a lokacin da lamarin ya faru - ikirarin da mahaifinsa ya goyi baya.
Daga bisani bayan zanga-zangar daga jami'iyun adawa da kuma kungiyoyin manoma, 'Yansanda suka kaddamar da bincike a ranar Litinin kuma ana tuhumar mahaifi da kuma ɗan sa.
"Nuna halin ko in kula da kuma jinkirin da 'yansanda suka yi wajen gabatar da koken abin ba abinda za a iya yi wa uzuri bane,'' in ji Vikram Singh, tsohon babban jami'in ɗansanda daga arewacin jihar a Uttar Pradesh.
"Abinda ya faru a Lakhimpur mafi muni ne saboda ya haddasa asarar rayuka, amma sai cafke dan Khan ya fi daukar hankali,'' a cewarsa.
Ayyukan kafafen yada labarai
A daukacin ranar Lahadi, wasu tashoshin talabijin sun mayar da hankulansu kacokan kan batun iyalan Khan. An dauki hotunansa da bidiyo lokacin da 'yansanda ke tasa keyarsa a ciki da wajen gine-ginen, kana ana rika nuna ''takardun umarnin cafke shi '' a kafofin talabijin kana aka rika yaɗawa a manahajar WhatsApp.
Wani mai gabatar da shirye-shirye ya rika bayyana cafke Khan a matsayin wani ''gagarumar bankadala ta taron sheke aya da dabdala'', a yayin da wani ya bukaci a kawo ''dangantaka tsakanin masana'antar Bollywood da kuma miyagun kwayoyi".
Bakin da aka a tattauna da su a tashar talabijin sun yi wasu ikirari marasa tushe game da ɗan tauraron fina-finan, kana suka soki lamarin shi da matarsa cewa sun gaza wajen tarbiyantar da ɗan su.
A shafin twaitter, sunan Aryan Khan ya shahara a kan wasu maudu'ai #BollywoodDruggies da #BollyDruggiesShamingNation - da ke alakanta masana'antar shirya fina-finan ta Bollywood da miyagun kwayoyi da kuma zubar da kimar kasa.
Amma fiye da sa'oi 24 bayan faruwar lamarin a Lakhimpur, har yanzu 'yansanda ba su gayyaci iyalan Mishra ba don amsa tambayoyi, kana kafofin talabijin sun yi tsit game da batun.
Dan 'fitaccen tauraro' da wanda ba sananne ba
Yaɗa labarai kan bankadar ta'ammali da miyagun kwayoyi sun kasance ''manyan batutuwa'', amma kuma sun zama ''abubuwan da ake tsammanin na aikinmu na yada labarai da za su fi jan hankulan jama'a da kuma neman suna,'' in ji tsohon ɗan jarida John Thomas.
"Darajar shaharar ɗan tauraron ne ya haddasa karkata wajen yada labaran da kuma tunanin irin abubuwan da akasarin mutane suka fi daukar hankali ko a kafar talabijin ko kuma jaridu,'' a cewarsa.
''Ta wani gefen, ɗan fitattacen ɗan siyasar wani ne da ba a san shi ba a faɗin ƙasar kamar mahaifinsa. Wa ya san da zaman karamin minista a gwamnatin Modi?"
Mista Singh ya ce bin kwakkwafi da yaɗa labarin wani ɓangare ne na ''boyayyiyar manufa, da wata hanyar zagon kasa'' don zubar da kimar masana'antar Bollywood.
Ya kuma yi nuni da batun tauraruwar Bollywood Rhea Chakraborty, wacce ta samu kan ta a tsakiyar mummunan al'amari na kalubale daga kafafen yada labarai a shekarar da ta gabata, wanda wasu fitattun 'yan jarida suka jagoranta, bayan da aka gano gawar saurayinta kuma tauraron fina-finai Sushant Singh Rajput, a dakinsa da ke birnin Mumbai a shekarar da ta gabata.
"Akwai wasu kwararan shaidu game da zarge-zargen da aka yi wa Rhea amma hakan ya zubar mata da kima.
Takardun neman izinin cafke Khan ba su nuna cewa an same shi dauke da miyagun kwayoyi ba, amma kuma kimar iyalansa ta zube,'' in ji shi.
"Laifi ne wanda za a iya neman beli, amma shin me yasa hukumar ta NCB ta bukaci a tsare shi?
Har ila yau, bai kamata a ce an bayyana wa jama'a ko wanene ake zargi ba, kana bai kamata a bari kafafen yada labarai su gano har su bayar da rahoto kan duk wasu al'amuransa bayan da aka cafke shi ba."
Yanayin yadda matasa ke shan miyagun kwayoyi" abin takaici ne ga bil'adama" , ya kara bayyanawa, tare da kiran mahukunta da su rika "yin tunani mai zurfi".