Matakai 12 da Jihar Katsina ta dauka don dakile matsalar tsaro

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ya sanya hannu kan dokar Shawo Kan Matsalolin Tsaro da niyyar magance wasu matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamna Aminu Masari kan yada labarai ya fitar a ranar Talata.
Dokar wacce za ta fara aiki a ranar 31 ga watan Agustan 2021, na ƙunshe ne da matakai 12 da suka haɗa da:
1. Haramta safarar shanu daga jihar Katsina zuwa kowace jiha a Najeriya.
2. Haramta daukar itace a manyan motoci daga cikin jeji.
3. Haramta sayar da dabbobi a kasuwannin kananan hukumomin Jibiya da Batsari da Safana da Danmusa da Kankara da Malumfashi da Charanchi da Mai'aduwa da Kafur da Faskari da Sabuwa da Baure da Dutsinma da kuma Kaita.
4. An haramta sayar da baburan da aka taba amfani da su a kasuwar Charanchi.
5. An hana daukar mutum uku a kan babur daya da kuma daukar fiye da fasinja uku a babur mai kafa uku wato Keke Napep.
6. Sannan dokar ta ba da umarnin rufe titin Jibiya zuwa Gurbi Baure inda motoci za su daina bi, sai su dinga bin hanyar Funtuwa a maimakonta har sai baba ta gani.
7. Ita ma hanyar Kankara zuwa Sheme an hana motocin haya bin ta, an kuma ba su shawarar su dinga bin hanyar Funtuwa. Sai dai an bai wa motoci masu zaman kansu umarnin bin hanyar idan suna bukata.

Wasu labarai masu alaƙa

8. Dokar ta kuma ƙayyade sayar da man fetur inda ba za a sayar wa masu ababen hawa na fiye da naira 5,000 ba a wasu ƙananan hukumomi 12.
9. Sannan a wasu gidajen mai biyu ne kawai da aka yarda a sayar da man, a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari da Safana da Danmusa da Faskari da Dandume da Musawa da Matazu da Dutsinma da Kurfi da Danja da kuma Kafur.
10. Sannan kuma an hana sayar da man fetur a jarka.
11. Kazalika dokar ta jaddada haramta zirga-zirgar babura da keke Napep daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a cikin birnin Katsina, sai kuma daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a ƙananan hukumomin jihar.
12. Sai dai kuma dokar ta bai wa ma'aikatan lafiya da 'yan jarida da jami'an tsaro damar amfani da babur da Keke Napep a lokutan da aka haramta din.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka fi fama da matsalolin tsaro da ake alakantawa da yan fashin daji a wannan lokaci.
Ko da a baya mahukunta a jihar sun sha daukar matakai iri daban-daban don daƙile barazanar da take fuskanta.
A baya-bayan nan ma gwamnan jihar ya shawarci 'yan jihar da su dauki makamai don kare kawunansu, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Duk da cewa mahukunta kan ce suna iya bakin kokarinsu don tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki, bayanai na nuna yadda ake samun karuwar hare-hare da satar mutane, abin da ke nuni da cewa har yanzu da sauran rina a kaba.












