Boko Haram: Abin da ya kamata ku sani game da 'yan bindiga masu wa'azi a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da bullar wasu bakin mutane a jihar, wadanda suka ce suna bin 'yan fashin daji suna yi musu wa'azi kan su daina kashe talakawan da ba su ji ba, ba su gani ba.
A wata tattaunawa da BBC Hausa, Wazirin Masarautar Dansadau, Alhaji Mustapha Umar, ya ce mutanen garin Dansadau da Dandalla sun shiga cikin firgici tun bayan bayyanar wadannan mutane.
Ya ce mutanen sun bulla a garin Dandalla, wanda bai wuce nisan kilomita goma daga Dansadau ba, a makon jiya.
A cewarsa "wadannan baki sun yi hudubar sallar Juma'a, suka yi nasihohi sannan suka bayar da sallah tare da jama'ar da ke cikin garin Dandalla."
Alhaji Mustapha Umar ya kara da cewa mutanen suna sanye da jallabiya kuma da alama su kansu 'yan bindigar suna jin tsoronsu.
"Yadda su [mutanen garin] suka siffanta min su [bakin] suna tsammanin 'yan Boko Haram ne domin sun ce baburansu akwai 'yan tutoci kuma suna dauke da kalmar shahada. Sannan a rigunansu akwai inda aka rubuta kamlar shahada." in ji shi.
Basaraken ya ce "tabbas mutanen suna yi wa 'yan fashin daji huduba na nuna cewa su daina zaluntar mutanen da suke zaune kusa da su a kauyuka; ya kamata a ce sun bar zaluntarsu su zauna tare da su girma da arziki.
Domin sun taba zuwa kusan shekara guda suka yi irin wannan batu da 'yan fashin dajin shi ya sa 'yan fashin suke tsoronsu. Sabon idan suka taho suna karanta musu ayoyin Alkur'ani suna yin fassara kan su zauna lafiya da mutanen da suke zaune kusa da su; idan har wani abu suke da niyyar yi, su rika yi dsa gwamnati."
Alhaji Mustapha Umar ya ce sun shaida wa hukumomi wannan lamari yana mai cewa "kuma idan irin shaidawar da aka yi bai kai kunnunwan mai daraja Gwamna ba, yanzu ga shi ina yin wannan bayani wanda nake fatan ya isa ga kunnensa da sauran mahukumanta."
Sharhi
Da ma masu sharhi kan lamuran tsaro irin su Abdu Bulama Bukarti sun sha bayyana cewa mayakan kungiyar Boko Haram da ke da sansanoni a arewa maso gabashin Najeriya sun mayar da hankalinsu a yankin arewa maso yammaci da ma tsakiyar kasar.
A watan Disambar 2020, kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon ɗaliban sakandiren Ƙanƙara da ke jihar Katsina da ta yi iƙirarin sace su ko da yake daga bisani hukumomi sun musanta hakan.
Kazalika a watan Afriliun da ya wuce, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce ƙungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu.










