Yadda 'yan kasashen Afirka ke tururuwar hakar zinare a Jamhuriyar Niger

Bayanan bidiyo, Bayanai sun nuna cewa akalla mutum 5000 daga kasashen yammacin Afirka ne suke tururuwa domin hakar zinare a gundumar Madarounfa

Akalla mutum dubu biyar daga kasashen Yammacin Afirka irin su Najeriya da Burkina Faso da Mali da sauransu ne suke tururuwa domin hakar zinare a gundumar Madarounfa da ke jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Allah ya albarkaci Nijar da ma'adinai daban-daban kamar su Uranium da man fetur da gawayi da sauran su.

Sannan abu na baya-bayan nan da aka gano a gundumar Madarounfa da ke jihar Maradi shi ne zinare.

Wannan ne ya sa tuni dubban jama'a daga kasashe makwabta suka ziyarci yankin tare da fara hakar zinariyar.

Wakilin BBC Abdou Halilou na daga cikin tawagar gwamnan jihar Katsinar Maradi, Alhaji Zakari Oumarou, a lokacin da ya ziyarci yankin.

Babban wuri ne mai fadin gaske kuma daga nesa za ka hangi laka ta shafe ko'ina sai kuma tarin kasa da ramuka da ake aikin hakar zinaren.

Idan ka matso kusa kuwa abu na farko da za ka fara ji shi ne surutu na daruruwan mutane dage yini cikin rana a nan.

Wadannan su ne masu aikin hakar zinare na yankin Madarounfa da ke jihar Maradi, a jamhuriyar Nijar.

Sani Abdou na daga cikin masu hakar zinariya a wannan wurin kuma ya ce tunda wani dan uwansu ya gano wajen aka yi masa cikar kwari.

"Wani dan uwanmu ne ya fara zuwa ya fara diba muka gani, ya saida ta Naira dubu 80 saboda mu nan munfi karfi kan Naira muka ji dadi duka 'yan garinmu suka yi cicirindo suka zo nan kuma kullum munatayi muna samu"

Wani mai hakar zinare
Bayanan hoto, Gwamnan ya ja kunnen masu hakar zinarin su guji lalata muhalli da kuma karya ka'idoji da aka shimfida na hakar zinari.

Baya ga masu aikin hakar zinarin, akwai kananan 'yan kasuwa da ke sayar da abinci da kayan sha da sauransu.

Sai dai baya ga alfanu da ake samu a mahakar zinarin masana na nuna fargaba kan lalacewar muhalli.

Dr. Ali Moumouni, malami a jimi'ar Dan Dikko Dan Koulodo da ke birnin Maradi, ya ce sun ga yadda ake lalata muhalli a wajen.

"Kafin mu iso ma sai da muka sauka muka zagaya saboda munga yadda laka ta toshe ko ina, muna gudun kar mutane musamman baki su zo da wasu sinadarai wadanda zasu sanya cikin ruwa da ake sha, ga damuna kuma mutane a tafki suke shan ruwa, kaga cuta zata kama mutane," in ji shi.

Shi kuwa gwamnan jihar Maradi Alhaji Zakari Oumarou, ya nemi a bi doka wajen aikin na hakar ma'adinai.

Gwamnan ya ja kunnen masu hakar zinarin su guji lalata muhalli da kuma karya ka'idoji da aka shimfida na hakar zinari.

Sannan ya ce nan gaba kadan za a bayar da takardun izini ga masu aikin hakar zinarin kamar yadda dokar kasar Nijar ta tanada.

Masu hakar zinare