Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabuwar cuta mai kama da Ebola ta bulla a Afirka ta Yamma
Jami'an kula da lafiya a Guinea sun tabbatar da mutuwar mutum na farko da ya kamu da kawayar cutar Marburg, wata cuta mai saurin yaduwa da kuma kisa, wadda take kusan iri daya da wadda take haddasa cutar Ebola.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce, dole ne a gaggauta tashi haikan domin dakatar da bazuwar cutar, wadda tuni ta hallaka mutumin da ta kama.
Ita dai wannan kwayar cutar ta Marburg wadda sunanta ya samo asali daga inda aka fara ganinta, a tarihi a wani dan karamin gari a yammacin Jamus, mai wannan suna Marburg a 1967.
Kwayar cuta ce da ke haddasa tsananin zazzabi, wadda kuma tana daga cikin mafiya hadari a duniya, domin tana iya kashe mutane cikin sati daya.
Jemage ne da ke cin 'ya'yan ita ce ke yada ta ga mutane, inda daga nan kuma sai ta fara bazuwa a tsakanin mutane, ta hanyar yawu ko jini ko kuma duk wani ruwa daga jikin mutum.
Cuta ce mai tsananin hadari wajen kisa, wadda ke sa zazzabi da ma zubar jini daga jikin mutum.
Abubuwan da aka diba daga jikin mutumin da ya fara kamuwa da ita a kasar ta Guinea, da ma Afirka ta yammar a yanzu,wanda tuni ya rasu, domin a yi gwaji, a dakunan bincike na kasar,sun tabbatar da cewa wannan kwayar cuta ce ta Marburg ta kama shi har ta yi sanadin mutuwar tasa.
Dr Matshidiso Moeti, ta Hukumar lafiya ta Duniya ta ce kwayar cutar na iya bazuwa kusan zuwa ko'ina.
A yanzu dai an shiga kokarin duba yadda za a gano mutanen da suka yi mu'amulla da marigayin.
Tsarin da aka yi amfani da shi a kasar ta Guinea da sauran makwabtan kasashe, wajen yaki da annobar Ebola a baya-bayan nan shi ne a yanzu ake sake dauka domin kare bazuwar ita wannan sabuwar kwayar cutar ta Marburg virus.
Ta bayyana ne yanzu bayan wata biyu kacal da ayyana Guinea a matsayin wadda babu sauran mai dauke da kawayar cutar Ebola.
Wannan shi ne karon farko da aka ga kwayar cutar a yankin Yammacin Afirka. Amma ta barke sau da dama a yankin kudu da kuma gabashin nahiyar ta Afirka a shekaru hamsin da suka gabata.