Watan Muharram: Muhimmancin watan farko na shekarar Musulunci

Al'ummar Musulmi na fara shiga watan Muharram ne a kowace shekarar Musulunci a matsayinsa na watan farko, wanda kuma yake da wasu keɓantattun ayyuka na ibada da tarihi.

Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Mai Alfarma Sa'ad Abubakar III ta bayyana Talata a matsayin ranar 1 ga watan na Muharram - wadda ta yi daidai da 10 ga watan Agustan 2021 - da kuma sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 bayan Hijirar Annabi Muhammadu SAW daga Makka zuwa Madina.

Ita ma Saudiyya ta ce Talata ce 1 ga sabuwar shekara saboda rashin ganin jaririn watan Muharram a ƙasar.

Ko watan na Muharram na da muhimmanci ko daraja ta musamman? Mun amsa wannan tambaya da ma wasu.

Mece ce ma'anar 'Muharram'?

Kalmar 'Muharram' wadda Larabci ce, na nufin wani abu mai tsarki ko kuma wanda aka tsarkake.

Saboda haka idan aka haɗa kalmar Muharram da kalmar 'shahru' - wato wata da Hausa - tana nufin wata mai tsarki.

Malamai sun ce Allah da kansa ya jingina wa kansa sunan watan a wani hadisi.

Watan Muharram na kamawa ne da zarar an yi sallar layya a ko kuma Idin Babbar Sallah a watan Zul-Hijja, inda Musulmai ke yanka dabbobi irin su raguna da shanu da raƙuma domin ci da kuma taimaka wa mabuƙata.

Mene ne muhimmancin watan Muharram a Musulunci?

Kasancewarsa wata na farko a kalandar Musulunci, ana kallon watan Muharram a matsayin wata alama ta mafarin sababbin abubuwa a sabuwar shekara.

Fitaccen malamin addini Sheikh Dr. Ibrahim Disina ya faɗa wa BBC Hausa cewa Muharram ɗaya ne cikin wata huɗu da suka fi alfarma (daraja) a shekarar Musulunci.

"Cikin huɗun ma shi ne [Muharram] ya fi su falala da matsayi kamar yadda ibn Rajab ya ambata," a cewar Malam Disina.

Ya ƙara da cewa shi ne wata ɗaya cikin watannin shekara guda 12 wanda Allah ya danganta shi zuwa gare shi a cikin Hadisi.

"Manzon Allah SAW ya faɗa da kansa cewa: Shaharullahlil Muharram [Watan Allah mai alfarma]."

Wane abu ake bukatar Musulmai su yi a Muharram?

Kamar yadda aka san wasu watannin Musulunci sun keɓanta da wasu ibadu, haka shi ma Muharram na da nasa abubuwan da ake buƙatar Musulmai su dinga yi.

Dr. Disina ya bayyana wasu na'ukan azumi a matsayin babbar ibadar da ake son a dinga yi. Su ne:

  • Yawaita azumi domin Annabi SAW ya ce: "Mafificin Azumi bayan azumin watan Ramadan shi ne azumi a watan Al-Muharram", Muslim ya rawaito.
  • Yin azumin ranar 10 ga watan Muharram (azumin Ashura) domin Annabi SAW ya ce: "Azumin Ashura yana kankare zunuban shekarar da ta gabata", Muslim ya rawaito.
  • Musulunci ya hana fara yaƙi a cikinsa ko kaima wasu farmaki.

Watannin Musulunci:

  • Muharram
  • Safar
  • Rabi'u Al-Awwal
  • Rabi'u Al-Thani
  • Jumada Al-Ula
  • Jumada Al-Thani
  • Rajab
  • Sha'aban
  • Ramadan
  • Shawwal
  • Zul-Kida
  • Zul-Hijja

Watannin Musulunci masu alfarma

Baya ga wata 12 da ake da su a kalandar Musulunci, akwai huɗu da ke da alfarma ko daraja ta musamman. Su ne:

  • Rajab
  • Zul-Kida
  • Zul-Hijja
  • Muharram

Ko Musulmai na yin bikin shiga sabuwar shekara?

Bikin shiga sabuwar shekara ya danganta da aƙidar da musulmi yake bi cikin ƙungiyoyin addinin Musulunci.

Duk da cewa wasu kan yi bikin, Dr. Ibrahim Disina ya ce a ilmance babu wani abu na biki da Shari'ar Musulunci ta tanadar na bukukuwa.

A cewarsa: "Amma a siyasance, wasu ƙasashe na ɗaukar wannnan rana da matsayi har sukan bayar da hutu a ƙasar saboda kamawarsa [Muharram]; kamar a Masar da Jordan da Kuwait da Qatar da sauransu, kamar yadda jihohin Kano da Oyo suka bayar da hutu don wannan rana."A Najeriya, ƙungiyoyin addini suna kiraye-kiraye ga gwamnati ta mayar da wannan ranar ta hutu kamar yadda ake yi a farkon shekarar miladiyya.