Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Teodoro Nguema Obiang Mangue: Dan shugaban ƙasa da ke ƙaunar Bugatti da Michael Jackson
- Marubuci, Daga Patrick Jackson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A cikin shekaru da dama tarin dukiyar Teodoro "Teodorin" Nguema Obiang Mangue su yi nuni da yanayin ƙasarsa Equatorial Guinea, yayin da ta bunkasa zuwa mafi girma a arzikin man fetur a yankin kudu da Saharar Afirka.
Ɗan shugaban ƙasa Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya more wata rayuwar jin dadi da wadata a birnin California da ƙasar Faransa.
Rayuwar jin dadinsa a ƙasashen waje sun yi matukar banbanta da na 'yan ƙasarsa, wadanda ba su ga komai a kasa ba a kuɗaɗen shiga da ƙasar ke samu daga arzikin mai.
Yanzu an bankaɗo yadda yake samun kuɗaɗen rayuwar holewar da yake yi a matsayin satar kudin kasa, bayan da aka yanke wa Teodorin hukunci kan aikata miyagun laifuka a ƙasar Faransa, da kuma aza masa takunkumi a Birtaniya, kana ga batun cin hanci da rashawa a Amurka.
Amma idan aka dawo gida ƙasarsa, mutum mai shekaru 52 na ci gaba da kasancewa mataimakin shugaban kasa, a matsayin wanda kuma zai gaji mahaifinsa mai shekaru 79.
'Tsananin satar kuɗi da tursasawa'
Teodoro ya zauna a jihar California tun a cikin 1991 lokacin da ya fara karatu a Jami'ar Pepperdine a birnin Malibu.
Daga bisani ne ya sayi wani babban gida na dala miliyan 30 a Malibu, da kuma sauran kadarori a Amurka da suka hada da motar alfarma ta Ferrari da kuma kayayyakin tunawa da shahararren mawaki Michael Jackson.
An yi wannan bandakalar ne a shekarar 2014 lokacin da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta tilasta masa mika kadarorinsa a matsayin biyan wasu kuɗaɗe bayan da aka gano cewa ya saye su ne ta hanyar ''cin hanci da rashawa''.
"Ta hanyar ci gaba da satar kuɗi da tursasawa, mataimakin Shugaban kasa Nguema Obiang ba tare da jin kunya ba, ya yi wa gwamnatinsa sata tare da yi wa harkokin kasuwancin ƙasarsa karan-tsaye don tallafawa rayuwarsa ta jin dadi da almubazzaranci, a yayin da 'yan kasarsa da dama ke rayuwa cikin kangin talauci,'' in ji Mataimakin Babban Alkali Caldwell a wata sanarwa.
Za a yi amfani da kuɗaɗen gwanjon kadarorin don amfanin mutanen ƙasar ta Equatorial Guinea".
'Babu sauran maɓoya'
A shekarar 2016, masu gabatar da kara na ƙasar Switzerland sun kwace motocin alfarma 11 mallakarsa. Cikin motocin da suka hada da Bugatti, da su Lamborghini, da su Ferrari, da su Bentley da kuma su Rolls Royce - an sayar da su a wani gwanjo na kusan dala miliyan 27.
Za a yi amfani da dala miliyan 23 wajen gudanar da wasu ayyukan kyautata jin dadin al'umma a ƙasar Equatorial Guinea.
Kana, a shekarar 2017 ne lokacin da ƙasar Faransa ta cafke Teodorin bayan da kotu ta same shi da aikata laifin sace kuɗin jama'a tare da bayar da umarnin ƙwace duka kadarorinsa a ƙasar.
An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku na gyara halinka ba tare da yana wurin zaman kotu ba, haɗe da tarar euro miliyan 30, kana aka ƙwace kadarorinsa na alfarma. Darajar daya daga cikin kadarorinsa da aka ƙwace a birnin Paris ta kai sama da dala miliyan 120.
A karkashin dokar ƙasar Faransa za a sake mallakawa 'yan ƙasar Equatorial Guinea wadannan dukiyoyi ne.
Babbar kotun daukaka ƙara ta dakatar da sakamakon hukuncin shari'ar, wacce ta yi watsi da bukatunsa na cewa ba shi da laifi, da kuma iƙirarinsa na cewa kotunan ƙasar Faransa ba su da hurumin yanke hukunci a kan kadarorinsa.
"Da wannan mataki... yanzu ƙasar Faransa ta daina kasancewa maɓoyar shugabannin ƙasashen waje da 'yan tawagarsu masu satar kuɗaɗen jama'a," in ji Patrick Lefas na ƙungiyar Transparency International ta ƙasar Faransa, wacce ke da ruwa da tsaki a kan shari'ar, a wata sanarwa (cikin harshen Faransanci).
Daga karshe, a makon jiya, Burtaniya ta garkama takunkumin yaƙi da cin hanci da rashwa kan Teodorin da sauran kusoshin gwamnatoci hudu daga ƙasashen Zimbabwe, da Venezuela da kuma Iraqi.
Burtniya ta ce tarin kayyakinsa na tunawa da Michael Jackson sun hada da safar hannun da aka lulluɓe da adon duwatsun alfarma ta dala dubu dari biyu da saba'in da biyar ($275,000) wacce mawakin ya taɓa sakawa a lokacin rangadin wakarsa ta ''Bad'' a shekarar 1980.
Takunkumin zai sa Burtaniya ta rufe asusun ajiyar bankuna da na bulaguro ga wadanda aka bayyana sunayensu, don haramta wa musu shigar da kuɗaɗe ta cikin bankunan Burtaniya da kuma shiga ƙasar.
Sakataren harkokin wajen Burtaniya Dominic Raab ya ce sabbin takunkuman a kan mutanen da ke ''cika aljihunsu da kuɗaɗen jama'ar ƙasarsu ne''.
Gargaɗi ga sauran mutane
Duk da ƙalubalen shari'ar a ƙasashen waje, Teodorin na ci gaba da riƙe matsayinsa na babbar kusa a cikin harkokin siyasar ƙasar Equatorial Guinea.
Mahaifinsa shi ne shugaban ƙasar da ya fi daɗewa a kan karagar mulki a ƙasashen Afirka, kana ƙungiyoyin kare hakkin bil adama na daukarsa a matsayin shugaban mafi girma a mulkin kama-karya.
Yayin da shi kan sa shugaban ƙasar babban kusa ne, dan sa ''sanannen mutum ne a yankunan yammaci da tsakiyar Afirka saboda jan hankulan kafafen yaɗa labaran kasa da kasa da ya yi", in ji wani mai sharhi a Afirka Paul Melly.
"Matakin da kotuna a wasu ƙasashen Turai suka ɗauka a kan zargin cin hanci da rashawa daga wasu iyalan shugabannin ƙasashen Afirka alama ce ta yiwuwar bacewar mutuntaka da kuma samun damar cin gajiyar kuɗaɗen tallafi da wasu gwamnatocin ƙasashen ka iya fuskanta," ya kara fada.
"Amma irin wadannan batutuwa ba su cika faruwa a yankin kudu da Saharar Afirka ba.''