Rikicin APC: Sabuwar takkadama na ruruwa a jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari.
Bayanan hoto, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara

A jihar Zamfara a Najeriya, tsohon gwamnan jihar Abdul'aziz Yari Abubakar ya yi watsi da sabon kwamitin rikon kwarya na mutum uku na jam'iyyar APC a jihar.

Tsohon gwamnan wanda a baya shi ne jagoran jam'iyyar a jihar Zamfara kafin daga bisani aka raba shi da mukamin bayan sauya sheka da gwamnan jihar na yanzu Bello Matawalle ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar ta APC.

Ya kuma soki shugaban riko na jam'iyyar na kasa kuma gwamnan Yobe Mai Mala Buni wanda ya kaddamar da kwamitin a Abuja.

Abdulazeez Yari ya ce rusa shugabancin jam'iyyar da kuma maya gurbinsa da kwamitin rikon kwarya saboda shigowar gwamna Mutawalle cikin APC ''babban kuskure ne wanda hankali ba zai dauka ba''

''Zan iya kai kara kotu kan rashin bin ka'ida''

Ya ce shugaban jam'iyyar na kasa, Mai Mala Buni bai da ikon sauya shugabancin kuma lamarin ka iya ''tayar da zaune tsaye.''

Wadanda aka nada a kwamitin rikon jam'iyyar a jihar ba 'yan jam'iyyar APC ba ne domin ''dukkansu babu mai katin jam'iyyar APC ko guda.''

Tsohon gwamnan ya ce muddin 'ya'yan jam'iyyar ba su hada kansu ba, to jam'iyyar za ta iya gamuwa da matsala. Don haka ya bukaci a maida hankali wajen kawo gyara a jam'iyyar a kuma kada a yi abin da zai iya ''rusa jam'iyyar.''

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce soke sahihancin rajistar 'yan jam'iyyar da ake ita da kuma yunkurin sabunta rajistar, ya saba kundin tsarin mulkin jam'iyyar kuma zai oiya zuwa kotu domin kalubalantar batun.

Martanin kwamitin shugabancin jam'iyyar APC a jihar Zamfara

To sai dai shugaban kwamitin rikon wanda aka dora wa aiki sasanta rikicin siyasar jihar da kuma sabunta rajistar 'yan jam'iyyar, Sanata Nasiha, ya musanta duka zarge-zargen rashin bin ka'ida.

Sanata Nasiha ya shaida wa BBC cewa muddin Abdulazeez Yari bai yarda da shugabancin kwamitin ba, to ''bai yarda da shugabancin jam'iyyar na kasa ba ke nan.''

Dangane da batun cewa su ba 'yan jam'iyyar APC ba ne, shugaban kwamitin ya ce shugaban rikon jam'iyyar na kasa Mai Mala Buni ya yi masu rajista kafin ya ba su aikin ''kuma shi ke da wuka da nama a hannunsa, ya yi mana rajista kafin ya ba mu takarda cewa mu je mu kama aiki.''

Ya kara da cewa babu wani bambanci tsakanin wanda yak e dan jam'iyya tsawon ''shekara hamsin'' da kuma wanda ya shigo a yau.

Matsayin uwar jam'iyyar APC ta kasa

Daya daga cikin manyan abubuwan da Shugaban rikon jam'iyyar na kasa, kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya maida hankali a kai a cikin watannin nan shi ne sasanta rikicin jam'iyyar a bangarori daban-daban da kuma kokarin jawo 'yan hamayya su shiga jam'iyyar. Ana shi kansa sauya shekar gwamnan jihar Zamfara daga PDP zawa APC sakamako ne na yunkurin uwar jam'iyyar ta kasa.

To sai dai rigingimu da hakan ya janyo na neman mayar da hannun agogog baya.

A dangane da takaddama ta baya-bayan nan a jihar Zamfara, uwar jam'iyyar ta kasa ta ce ba ta saba wa ka'idodjin jam'iyya ba kuma dukkan matakan da aka dauka an yi ne domin a samu maslaha.

Malam Salisu Na`inna Danbatta , Daraktan Yada labarai na Jam`iyyar APC a Najeriya, ya ce kafin a rusa shugabancin jam'iyyar a jihar Zamfara kana a kafa kwamitin riko bayan sauya shekar Gwamna Matawalle, ''an tuntubi duk wadanda su ke da ruwa da tsaki''

Wakilin BBC Awwal Janyau ya ce wannan rigima babban kalubale ne ga jam'iyyar APC a jihar Zamfara gabanin manyan zabukan 2023.