EFCC ta ƙaddamar da manhajar fallasa cin hanci da rashawa a Najeriya

EFCC

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto, EFCC ta ce ba za ta daina karɓar ƙorafe-ƙorafe ta hanyar da ta saba ba

Hukumar da ke Yaki da Cin Hanshi Hanci da Rashawa a Najeriya, EFCC, ta kaddamar da wata manhaja da za ta ba 'yan kasar damar daukar hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, wanda ya kaddamar da manhajar Eagle Eye a Abuja ranar Laraba, ya bayyana wa manema labarai yadda ake sauko da ita daga manyan rumbunan manhajoji na wayar salula.

Da yake magana da BBC Hausa jim kaɗan bayan taron, Abdulrasheed Bawa ya ce yunƙurin nasu yana cikin shirin nan na kwarmata bayanai da ake Whistle Blower a Ingilishi.

"Duk wanda yake so ya kwarmata mata bayanai don ya samu wani abu zai iya yin hakan a ciki kuma ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na mai kwarmata bayanai," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa mutum zai iya ɗaukar hoton gidan da ake aikata laifin rashawa da kuma adireshinsa ya turo musu, "mu kuma sai mu bincika".

Yadda manhajar Eagle Eye ke aiki

Abdulrasheed Bawa,
Bayanan hoto, Abdulrasheed Bawa ya ce masu amfani da wayoyin Apple da Android duka za su iya amfani da Eagle Eye

Abdulrasheed Bawa, mai shekara 40 wanda ya zama shugaban hukumar a watan Fabarairun 2021, ya ce ana iya samun manhajar a App Store ga masu wayoyin Apple da kuma Google Play Store ga masu amfani da Android.

Ya ce: "Wannan manhaja tamu sunanta Eagle Eye. Za ku ga bajonmu na EFCC kamar yadda aka san shi. Idan aka duba App Store ko Google Play Store za a gan ta da suna Eagle Eye kuma za a ga EFCC a jiki.

"Idan aka sauke ta za ta yi aiki ne kamar yadda Facebook ko WhatsApp yake a waya. Duk lokacin da kake son yin amfani da ita za ka buɗe ne kawai ka fara.

"Mutum zai iya ɗaukar hoton gidan [da ake aikata laifin rashawa] da kuma adireshinsa ya turo mana mu kuma sai mu bincika. Idan ya ga dama ya faɗa mana sunansa, idan bai ga dama ba kuma shikenan."

Sai dai shugaban ya gargaɗi masu kwarmata bayanai cewa dole ne su tabbata cewa bayanan da za su bayar na gaskiya ne.

"Idan mutum ya faɗa mana bayanai za mu gayyace shi ya zo ya cike wasu takardu sannan kafin a fara za mu faɗa masa cewa idan muka gano bayanan nasa ƙarya ne, yana yi ne don tozarta wani, to shi ma fa hannun doka zai kama shi," in ji shi.

Mene ne shirin kwarmata bayanai na Whistle Blower?

Jami'an EFCC

Asalin hoton, EFCC

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin kwarmata bayanai a shekarar 2016 da zummar bai wa ma'aikaata da ɗaiɗaikun mutane damar fallasa ayyukan cin hanci da rashawa, ita kuma gwamnati ta saka musu da kuɗi.

A cewar Ministar Kuɗi ta lokacin, Kemi Adosun, babbar hikimar ɓullo da shirin ita ce taimaka wa yaƙi da rashawa ta hanyar yawaita bankaɗo laifukan da kuma bai wa masu bankaɗowar lada.

A watan Maris na 2020, shugaban kwamitin da ke bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaƙi da rashawa na Presidential Advisory Committee against Corruption (PACAC) ya ce sun ƙwato naira biliyan 594.09 ta hanyar shirin tun bayan ƙaddamar da shi.

Farfesa Itse Sagay ya ce shirin ya ƙirƙiro hanyar bai wa masu kwarmata bayanai lada da ya kai kashi 2.5 zuwa 5.0 cikin 100 na jumillar adadin kuɗin da aka yi almundahanarsu matuƙar suka taimaka da bayanai.

"Shirin ya yi nasara matuƙa ba wai ta hanyar ƙwato kuɗaɗe ba kawai, har da samun bayanan hanyoyin da masu laifi ke bi wajen aikata su," a cewarsa.