JAMB: Hukumar shirya jarrabawar ta ce babu hujjar cewa an yi mummunar faɗuwa a 2021

Tun bayan da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta saki sakamakon 2021 mutane ke ta cewa ɗalibai sun yi mummunar faɗuwa musamman a arewacin Najeriya.

Mutane da dama sun yaɗa sharhi iri-iri a shafukan zumunta game da dalilan da suka jawo mummunar faɗuwar ɗaliban.

Wasu ma na iƙirarin cewa kashi 10 cikin 100 ne kacal suka ci maki 200 ko fiye a jarrawabar, wadda aka gudanar a ranakun 19 da 22 na watan Yuni.

Hukumar Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) ta saki sakamakon ne ranar Juma'a 25 ga Yuni na ɗaliban da suka rubuta ta a cibiyoyin komfuta fiye da 720 a faɗin Najeriya.

'Babu hujjar da ke nuna mummunar faɗuwa'

Hukumar JAMB ta tabbatar wa da BBC Hausa cewa alƙaluman da mutane ke ambatowa na mummunar faɗuwa ba daga wajenta suke ba.

Duk da cewa ta saki sakamakon da ke nuna wa kowane ɗalibi abin da ya samu, sai dai ba shi ne abin da zai tantance yin nasara ko faɗuwa ba a jumlace.

"A matsayinmu na hukumar da ke kula da wannan jarrabawar, ba mu fitar da waɗannan bayanan ba," a cewar mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin, yayin da BBC ta tuntuɓe shi ta wayar tarho.

Ya ƙara da cewa mutane ne kawai suke yaɗa jita-jita "saboda ba su ci jarrabawar ba".

A cewarsa: "Da ma haka mutane suke; idan mutum bai ci jarrabawa ba kawai sai su fara yaɗa tunaninsu. JAMB ba jarrabawa ce da ake cewa an ci ko an faɗi ba kai-tsaye saboda sakamakon da wani yake buƙata ya shiga jami'a ba shi wani ke buƙata ba."

A 2013 ne hukumar JAMB ta ƙaddamar da rubuta jarrabawar ta komfuta amma sai a 2015 aka mayar da tilas ga duk ɗlibin da ke son shiga jami'a ko kuma wasu kwalejoji.

Ta yaya za a san an yi mummunar faɗuwa ko nasara?

A kodayaushe, ana iya sanin babbar nasara ko mummunar faɗuwa ne idan JAMB ta fitar da jadawali na bayan da jarrabawar, waɗanda ke fayyace ƙoƙarin ɗaliban kowace jiha ko yanki a Najeriya a jumlace.

Da BBC ta tambaye shi ko sun saki alƙaluman na jarrabawar 2021, Mista Benjamin ya ce: "A'a, sai nan gaba za a fitar, zan turo muku."

Ta cikin waɗannan alƙaluma ne za a zayyana kashi nawa ne suka ci maki mafi yawa ko kuma waɗanda suka ci mafi ƙaranci.

Hukunci

Bisa bayanan da ake yaɗawa a shafukan zumunta, mutane kan ce maƙotansu ko 'yan unguwarsu da yawa ba su ci JAMB ba.

Sai dai wannan ba zai zama hujjar cewa an yi mummunar faɗuwa ba, musamman idan aka kwatanta yawan ɗalibai na ɗaiɗaikun jihohin Najeriya.

A taƙaice dai, iƙirarin da mutane ke yi cewa ɗalibai sun yi mummunar faɗuwa a jarrabar JAMB ta 2021 a Najeriya ko wani ɓangare ba shi da wani tushe saboda babu alƙaluman da ke tabbatar da hakan.