2021 Jamb UTME: Yadda za ku duba sakamakonku na jarrabawar ta bana

Asalin hoton, JAMB/FACEBOOK
Har yanzu ba a saki sakamakon jarrabawar JAMB ba ta shekarar 2021 kamar yadda hukumar da ke shirya jarrabawar ta sha alwashin yi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa za a fitar da sakamakon jarrabawar wannan shekarar a ranar 23 ga watan Yuni.
Game da wannan rahoto, NAN ya ce, "Shugaban hukumar Ishaq Oloyede ne ya bayyana cewa za a saki sakamakon ne a ranar Laraba, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Enugu.
"Ya kamata a ce sakamakon ya fita ya zuwa yanzu, amma saboda ba na hedikwata shi ya sa ba na son na bayar da umarnin fitar da sakamakon lokacin ba na kusa," in ji rahoton.
Daga baya BBC ta tuntubi kakakin hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin, ta wayar tarho inda ya ce ba shi da masaniya kan sakin sakamakon a ranar 23 ga watan Yuni.
Fabian ya ce za su jira shugaban ya koma hedikwatar hukumar da ke Abuja kafin ya tabbatar da labarin.
Duk da haka amma za mu ci gaba da bibiyar wannan labari domin kawo wa daliban da suka yi jarrabawar labari kan sakamakon na 2021.
Amma a gefe guda kuma ga yadda dalibai za su iya duba sakamakon su kuma cire takardarsu ta ainihi.

Asalin hoton, Facebook/JAMB
Yadda za a iya duba sakamakon JAMB a intanet
- Da farko mutum zai fara shiga wannan shafin wanda shi ne na JAMB https://portal.jamb.gov.ng/eFacility_/CheckUTMEResults
- Sai a sanya lambar JAMB da kuma Email din dalibin a wurin da ake bukaci hakan
- Sai ka danna neman sakamako
- Shafin zai fara nemo maka sakamakon.
Yadda za a iya duba sakamakon ta hanyar tura sakon waya
- Dalibin da ya zana JAMB zai tura sakon RESULT zuwa lambobi 55019 da lambar wayar da ka yi rijistar JAMB da ita
- Idan kuma aka tura sakon da lamba daban da ba da ita dalibi ya yi rijista ba, sakon da zai zo, zai zo ne a wani mataki na daban
- Dalibin da ya yi rijista zai ga sakonshi ya iso: "Zuwa ga wane/wance sakamakon shi ne.... (sai kuma a ga sakamakon)
- In kuma JAMB ta rike sakamakonka za a aiko sako ya ce "An rike sakamakonka"
In kana da bukatar cire sakamakon jarrabawarka, ga mataki mai sauki da za ka iya bi, kamar yadda aka wallafa a shafin JAMB, sai dalibi ya biya naira 1,000 zai iya samun damar fitar da sakamakon nasa.
Yadda za ku iya sauke sakamakonku na ainihi daga intanet
Shigar da bayananka a shafin JAMB https://www.jamb.gov.ng/EfacilityLogin
Karkashin jerin bayanan da za ku bude za ku daga Registration e-Facilites daga bangaren hannun hagu, sai kuma ku danna cire sakamako.

Asalin hoton, Jamb
Sai ka danna "ci gaba da shirin biyan kudi" sai a biya kudin ta hanyar Remita.
Bayan ka biya kudin kamar yadda ya kamata, to daga nan zaka iya cire sakamakonka, sai ka zabi shekarar da ka zana jarrabawar, sai kuma a sanya lambar JAMB a inda aka bukata.
Sai dalibi ya gabatar da sakamakon jarrabawarsa ta ainihi a yayin tantancewa lokacin shiga makarantun gaba da sakandire.
Me JAMB ke cewa a game da wadanda ba su zauna jarrabawar 2021 ba?
Shigar da kokenka a shafin JAMB a wurin da aka rubuta e-ticket.
Da yawa daga cikin ma'aikatan hukumar na taimakawa wajen warware matsaloli.
Duk dalibin da ke korafin zuwa a makare sakamakon dokar hana fita da aka sa a yankinsu za a iya shawo kansu.
Sai a shiga e-ticket a shafin domin shigar da korafi a hukumance.
An kirkiri wannan wajen ne domin bayar da dama a shigar da korafi.
Kuma ana bibiyar ƙorafe-ƙorafen a kan lokaci.
Za a iya aika sakon kar ta kwana zuwa 55019 domin shigar da wannan ƙorafi.











