An kama wani mawaƙi bisa zargin ridda a Kano

Bayanan bidiyo, 'Abin da ya sa muka kama mutumin da ake zargi ya yi ridda a Kano'

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS, ta ce ta kama wani mawaki bisa zargin yin kalaman batanci ga Allah (SWT) a cikin wata waka.

Hukumar ta DSS ta shaida wa BBC Hausa cewa an kama mawakin Ahmad Abdul, mai shekara 35, bayan ya fitar da wakar ba tare da hukumar tace fina-finai da dab'i ta Jihar Kano ta tantance ta ba.

An tsare matashin ne domin kauce wa tashin hankali da kai wa matashin da iyayensa hari a sakamakon wakar da ya yi, a cewar DSS.

Sai dai ta kara da cewa matashin ya amsa laifinsa bayan hukumar tace fina-finan ta Kano ta nuna masa illar abin da ya yi.

Jami'an hukumar ta DSS sun shaida wa wakilin BBC a Kano cewa mawakin ya "nemi afuwar al'ummar jihar da daukacin Musulmin duniya kan wakar da ya yi"

Kazalika, mahaifan matashin sun yaba wa DSS da hukumar tace fina-finai bisa ga wannan mataki da suka dauka.

Hukumar ta bayar da belinsa bayan ya nemi afuwa.

jami'an hukumar DSS

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jami'an hukumar DSS sun shaida wa wakilin BBC a Kano cewa mawakin ya "nemi afuwar al'ummar jihar da daukacin Musulmin duniya kan wakar da ya yi"

A watan Agustan 2020 wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wani matashi Yahaya Aminu Sharif, mai shekara 22, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

Tun a watan Maris na shekarar ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge shi da yin ɓatancin a cikinta.

Hakan ya sa matasa sun yi zanga-zanga a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda suka nemi a hukunta shi.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa sun far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai kuma suka lalata duk abin da ke ciki.