Muhammadu Buhari: Abubuwan da shugaban Najeriya ya yi a ziyararsa ta Borno

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis.

Shugaban na Najeriya ya isa filin jirgin saman Maiduguri da safiyar ranar ta Alhamis kuma daga nan ya shiga aiwatar da abubuwan da suka kai shi jihar.

Wata sanarwa da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Isa Gusau ta ce Shugaba Buhari ya bayyana cewa 'na yi matukar jin dadi' bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin ayyuka 556 da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Shugaba Buhari ya yi tsokaci na musamman kan Makarantar Koyon Ayyukan Hannu da ya kaddamar a Muna, wadda ya bayyana a matsayin wata cibiya da za ta samar da ayyukan yi da kuma rage zaman kashe wando ga matasa ta yadda zai yi wahala kungiyar Boko Haram ta dauke su, a cewar Isa Gusau.

An tsara makarantar ce domin mutum 1,500 su samu horon sana'o'i a duk shekara, in ji gwamnatin ta jihar Borno.

Shugaban kasar ya kai ziyara wurare da dama ciki har da sansanin sojoji da sauran jami'an tsaron da ke rundunar Operation Hadin Kai wadda take yaki da 'yan Boko Haram.

A jawabinsa ga sojojin, Shugaba Buhari ya jinjina musu bisa sadaukarwar da suke yi wajen ganin an tabbatar da tsaron Najeriya.

"Ina mika ta'aziyyata ga iyalan sojojin da suka riga mu gida gaskiya kuma ina yi musu addu'ar neman gafara, sannan ina mai tabbatar muku cewa gwamnatina za ta yi duk mai yiwuwa domin kula da mata da 'ya'yan sojojin da suka mutu," in ji Shugaba Buhari.

Ya yi kira a gare su da kada su bari 'yan ta'adda su ci karfinsu, yana mai shan alwashin ci gaba da bayar da dukkan abubuwan da suka kamata wajen ganin ayyukansu sun tafi yadda suka dace.

Wakilin BBC da yanzu haka yake Maiduguri, Ibrahim Isa, ya ce dimbin mutane ne suka fita domin tarbar shugaban na Najeriya.

Da ma dai Gwamna Babagana Umara Zulum ya roƙi ƴan jihar da su ba da goyon baya da fatan alheri a yayin ziyarar.

"Ina sake gode muku kan goyon bayan da kuka bai wa gwamnatin nan. Ina godiya ga kowa da kowa, kan goyon bayanku da fatan alherinku da addu'o'i da kuma zamantowarku ƴan ƙasa na gari," kamar yadda sanarwar ta ce.

Ihun da aka yi wa Buhari a bara

A watan Fabrairun 2020 ne Shugaba Buhari ya kai ziyara Borno, inda har wani dandazon mutane suka yi wa shugaban ihun ''ba ma yi, ba ma yi''.

Hakan kuma ya faru ne lokacin da Buhari yake barin fadar Shehun Borno zuwa gidan gwamna a wani waje da ake cewa 'Yan Nono.

A wancan lokacin Buhari ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa hare-haren da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Sai dai kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce wanda ya dauki bidiyon da ya bazu a shafukan intanet da ke nuna ana yi wa Buhari ihu bai a yi wa mutanen Borno adalci ba — wadanda ya ce an san su da karamci da son baki.

"Da ni aka shiga gari [Maiduguri] tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Shehun Borno kuma jama'a ne suka fito suna cewa sun gode suna ala san barka."

"Amma akwai wata matattara da suke cewa ba sa so, kuma ni ma na ji da kai na masu cewa ba sa so," in ji Garba Shehu.