IPOB: Hotunan yadda kiran IPOB ya yi tasiri a jihohin Igbo

Shugaban ƙungiyar IPOB, mai fafutukar ɓallewa daga Najeriya Nnamdi Kanu ya bai wa al'ummar yankin Ibo umarnin zama a gida yau litinin don tunawa da mutanen da aka kashe a yaƙin basasar Najeriya.

IPOB Curfew
Bayanan hoto, A jihar Enugu makarantu da ofisoshi da kasuwanni duk sun kasance a rufe
IPOB Curfew
Bayanan hoto, Tituna a yankuna da dama na kudu maso gabashi da kudu maso kudancin Najeriya sun kasance babu zirga-zirga sakamakon umarnin da kungiyar IPOB mai fafutukar ɓallewa daga kasar ta bayar na cewa kowa ya zauna a gida
IPOB Curfew
Bayanan hoto, Gwamnatocin yankin dai sun bukaci jama'a su yi watsi da umarnin inda suka ce kowa ya fita ya yi harkokinsa, sai dai a wurare da dama jama'a basu fita ba
IPOB Curfew
Bayanan hoto, Mutane sun ƙi fitowa saboda gudun abin da zai je ya dawo a jihohin Kudu maso gabashin Najeriya da dama
IPOB Curfew
Bayanan hoto, Duk ranar 30 ga watan Mayu jihohin kudu maso gabashin Najeriya suka ware don tunawa da ƴan ƙabilar Ibo da aka kashe a yaƙin basasar Najeriya da aka yi tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 wanda Janar Odumegwu Ojukwu ya assasa
IPOB Curfew
Bayanan hoto, Wasu rahotanni na bayyana cewa Ƴan Sanda a jihar Ebonyi sun harbe wani mutum bayan da suka kama shi da wasu makamai a wani gida da mayaƙan IPOB ke zama
IPOB Curfew
Bayanan hoto, A jihar Enugu makarantu da ofisoshi da kasuwanni duk sun kasance a rufe
IPOB Curfew
Bayanan hoto, A jami'ar jihar Ebonyi ma, ajujuwa sun kasance a kulle sai jami'an tsaro kawai da ke sintiri a faɗin jami'ar
IPOB Curfew
Bayanan hoto, Kungiyar IPOB dai ta bayar da umurnin ne don tunawa da ranar fafutukar da suke yi na kafa kasarsu da kuma tunawa da gwarazan mayakansu da suka mutu a gwagwarmayar

Haƙƙin mallakar hotuna na BBC