Ibrahim Attahiru: Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya rasu

I A Attahiru

Asalin hoton, NIG ARMY FACEBOOK

Lokacin karatu: Minti 2

Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hadarin jirgin saman soji a Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Mohammed Yarima ne ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.

Bayanai sun ce jirgin saman na soji ya fadi ne a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Kaduna kuma mutum takwas ne a cikin jirgin lokacin da lamarin ya faru.

Rundunar sojin saman Najeriyar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twiiter inda ta bayyana cewa wani jirginta ya faɗi a kusa da filin jirgin sama na Kaduna.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ta kuma ce tana bincike kan abin da ya haifar da haɗarin.

Wane ne Janar Attahiru?

Manjo Janar Attahiru

Asalin hoton, Presidency

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai babban hafsan sojan ƙasa.

An haifi Janar Attahiru a 1966 a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Ya taba jagorantar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga muƙamin bayan wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.

Kafin ba shi wannan muƙamin, Laftanar Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin Najeriya.

Ranar 26 ga watan Janairun 2021 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin Babban Hafsan Sojin ƙasar.

Janar Attahiru shi ne babban Hafsan Sojin Najeriya na 21.

Short presentational grey line

Wannan ne haɗarin jirgin sojin saman Najeriya na uku cikin wannan shekarar ta 2021.

A watan Janairu wannan shekarar ma wani jirgin rundunar ya faɗi a kusa da filin jirgin sama na Abuja babban birnin Najeriya.

Haka kuma, ran 31 ga watan Maris rahotanni suka bayyana cewa akwai jirgin rundunar da ya yi ɓatan dabo a jihar Borno, kuma bayan ƴan kwanaki rundunar ta sanar da cewa akwai yiwuwar jirgin nata faɗuwa ya yi.

Kawo yanzu ba a ga jirgin ba.