Hajj 2021: Saudiyya ta ce mahajjata 60,000 ne za su yi aikin Hajjin bana

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Saudiyya ta ce mahajjata 60,000 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga fadin duniya.
Hukumar masallatai biyu masu daraja Haramain ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce mutum 45,000 za a bai wa dama daga kasashen duniya su yi Hajjin, a kuma bai wa 15,000 daga cikin Saudiyya.
Ta kuma ce ta fitar da bayanan dokoki da tsare-tsare mai shafi tara a kan wannan mataki, kan yadda za a gabatar da aikin Hajjin cikin dokokin dakile cutar korona.
Dama a ranar Juma'a Saudiyya ta fitar da sanarwar farko cewa za a bar maniyyata daga fadin duniya su je aikin Hajji a wannan shekarar.
An dauki wannan hukunci ne bayan da hukumar Hajji da Umara ta kasar ta yanke shawara a ranar 9 ga watan Mayu cewa ya kamata a bar mahajjata su yi aikin amma da sharudan hukumomin lafiya.
A farkon wannan watan ne, Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta ce za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kiyaye lafiyar duk wanda ya je aikin ibada a kasar.
Tun kafin wannan sanarwar kasashe irin su Najeriya ke sa rai tare da fatan za a bar maniyyatanta zuwa Hajjin na bana.
Musulmai sama da miliyan 2.5 ne ke zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji a ko wacce shekara daga fadin duniya.
Amma saboda annobar korona aka rage adadin zuwa 1,000 a bara, kuma su ma mazauna Saudiyyan ne kawai.
Annobar cutar korona ta janyo an samu sauye-sauye da dama na yadda ake gudanar da ibada a Makka da Madina kamar shiga sallah Harami da Dawafi da Safa da Marwa da sauran su.
Karin labarai masu alaka

Asalin hoton, Getty Images











