INEC: Ofisoshin hukumar zaben Najeriya da suka kone daga 2019 zuwa 2021

INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriya ta yi gargadi cewa yawan kona ofisoshinta da ake yi a baya-bayan nan na barazana ga shirin zabukan shekarar 2023.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yana mai cewa ya yi amannar yanzu kam saka wutar ake yi ba tsautsayi ne ba.

Ana ci gaba da samun tashin gobara a ofisoshin INEC a fadin kasar, musamman a kudanci, inda zuwa yanzu aka kona 22 tun daga shekarar 2019.

Lamari na baya-bayan nan da ya faru shi ne na konewar ofisoshin INEC biyu a jihar Ebonyi ranar Talata da daddare.

An yi asarar kayayyakin aiki da dukiyoyi kamar motoci da sauransu a kusan dukkan hare-haren. Kazalika ya jawo tsaiko ga ci gaba da bayar da rijistar zabe da ake yi a wasu wuraren

Ga dai jerin ofisoshin da aka kona da jihohinsu:

  • Ofishin karamar hukumar Ebonyi a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabas - Talata 18 ga watan Mayun 2021
  • Ofishin karamar hukumar Ezza a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabas - Talata 18 ga watan Mayun 2021
  • Babban ofishin jihar Enugu a kudu maso gabas - Lahadi 16 ga watan Mayun 2021
  • Ofishin INEC da ke Obollo-Afor a karamar hukumar Udenu, jihar Enugu a kudu maso gabas - Alhamis 13 ga watan Mayun 2021
  • Ofishin INEC na karamar hukumar Ohafia da ke jihar Abia a kudu maso gabas - Lahadi 9 ga watan Mayun 2021
  • Ofishin karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa-Ibom da ke kudu maso kudu - Lahadi 2 ga watan Mayun 2021
  • Wani bangare na babban Ofishin INEC na jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya - 21 Afrilun 2021
  • Ofishin INEC na karamar hukumar Orlu a jihar Imo da ke kudu maso gabas - Watan Fabrairun 2020
  • Ofishin INEC na Ogidi a karamar hukumar Idemili ta Arewa - Fabrairun 2020
  • Ofishin karamar hukumar Aba ta kudu a jihar Abia da ke kudu maso gabas - 13 ga watan Disamban 2020
  • Ofishin karamar hukumar Arochukwu a jihar Abia da ke kudu maso gabas - Watan Oktoban 2020
  • Babban ofishin INEC da ke birnin Akure na jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya - Satumban 2020
  • Ofishin karamar hukumar Ngor Okpala a jihar Imo da ke kudu maso gabas - Watan Maris 2020
  • Ofishin INEC a babban birnin tarayya Abuja - Watan Afrilun 2020
  • Ofishin INEC na karamar hukuma Oyigbo da ke jihar Rivers a kudu maso kudancin Najeriya - Janairtun 2019
  • Ofishin INEC na karamar hukumar Qua'anpan a jihar Filato yankin tsakiyar Najeriya - Fabrairun 2019
  • Ofishin karamar hukumar Isiala Mbano a arewacin jihar Imo da ke kudu maso gabas - Watan Fabrairun 2019
  • Ofishin INEC na jihar Anambra da ke kudu maso gabas - Fabrairun 2019
  • Ofishin INEC na karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa, arewa maso yammacin Najeriya - Mayun 2019
  • Ofishin karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar Akwa-Ibom da ke kudu maso kudu - A shekarar 2019
  • Ofishin karamar hukumar Mkpat Enin a jihar Akwa-Ibom da ke kudu maso kudu - A shekarar 2019
  • Ofishin karamar hukumar Eastern Obolo a jihar Akwa-Ibom da ke kudu maso kudu - A shekarar 2019
Shugaban Inec Mahmoud Yakubu

Asalin hoton, Getty Images

Ko a ranar 18 ga watan Mayun 2021 ma sai da matsalar tsaro ta sa hukumar INEC din kiran wani taron gaggawa na jami'anta da ke jihohi, da na wani kwamitin musamman kan harkokin tsaro, bayan hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshinta a yankin kudu maso gabas.

Daraktan wayar da kan jama'a na hukumar ta INEC Mista Nick Dazeng, ya shaida wa BBC cewa irin wannan hari shi ne na uku da aka kai wa hukumar, abin da ke janyo barazana ga zabukan 2023.

"Mun shaida wa jami'an tsaro dukkanin abubuwan da ke faruwa game da hare-haren da ake kai wa ofisoshinmu domin su gudanar da bincike don gano ko su wane ne suke yin wannan ta'asa, sannan ranar Larabar nan za mu gana da shugabannin hukumar zabe don tattauna batun" in ji Dazeng.

Ya kara da cewa kafin karshen mako hukumar za ta kara zaunawa da kwamitin tsaro na Najeriya domin lalubo mafita game da al'amarin.