Majalisar Dattawan Najeriya na son a ɗaure duk wanda ya biya kuɗin fansa shekara 15 a gidan yari

Majalisar Dattawa

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar Dattawa a Najeriya na son a haramta biya da karɓar kuɗin fansa da niyyar kuɓutar duk wani da aka yi garkuwa da shi.

Haka kuma majalisar ta nemi a yanke wa duk wanda aka kama ya biya ko ya karɓi kuɗin fansa hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari.

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da kudirin na 2021 mai taken 'magance ayyukan ta'addanci kuma sanarwar ofishin shugaban majalisar dattawan ya fitar ta ce kudirin yanzu ya tsallake karatu na biyu.

Idan kudurin ya zama doka, hukuncin biyan kuɗin fansa za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.

Da yake jagorantar muhawara kan kudurin, dan majalisar ya ce, "dokar ta'addanci ta 2013 tana bukatar gyara don haramta biyan kudin fansa ga masu satar mutane domin sakin duk wani wanda aka sace ko tsare shi bisa kuskure.

A cewar Onyewuchi, kudirin dokar na neman maye gurbin sashi na 14 na Babban Dokar a matsayin wani sabon sashi kamar haka: "Duk wanda ya tura kudade, ya biya ko kuma ya hada baki da wani mai satar mutane ko kuma ɗan ta'adda don karbar kuɗin fansa da niyyar don sakin wani wanda aka sace ko aka tsare ko ɗaure shi to ya aikata babban laifi kuma zai iya ɗaukar hukuncin ɗaurin shekaru 15. "

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa yanzu satar mutane ta zama babban kasuwancin da ke kawo kudi mai yawa cikin sauri, yana mai cewa, "yanzu haka ya kasance mafi munin ta'addanci da ake aikatawa wanda kuma ke ƙara girma a kasar."

Ya ce yadda ake yawan satar mutane a Najeriya ya jefa ƴan ƙasar cikin tsoro da fargaba.

Ya bayar da misali da ƙasashe kamar Amurka da Ingila da ke kyamar biyan kudin fansa ga masu satar mutane.

Onyewuchi ya ce "Biyan kudin fansa ga 'yan ta'adda ya saɓa dokar ta'addanci ta Burtaniya ta 2000 kamar yadda Amurka ke bin tsarin kaucewa biyan kuɗin fansa ga ƴan ta'adda."

Sanarwar ta kuma ambato ɗan majalisar na cewa "satar mutane na karuwa a Najeriya kuma yanzu ta zama ruwan dare a dukkan sassan Najeriya.

"Wasu na ganin matsalar na ƙaruwa ne saboda talauci da matsalar addini da siyasa da ƙarancin dokokin da ake da su da rashin aikin yi da cin hanci da rashawa, da kuma son kai da sauransu.

"Matasan mu marasa aikin yi sun faɗa satar mutane don neman kudn fansa a matsayin wata hanyar samun abinci."

Don a haka cwar ɗan majalisar bai gaba da a ƙarfafa biyan kudin fansa ba, abin da ya fi dacewa shi ne gwamnati ta samar da tsaro da karfafa tattalin arziki cikin gaggawa.

Sannan gwamnati ta bunƙasa shirye-shiryenta na rage raɗaɗin talauci da samar da ayyukan yi ga matasa wadanda galibi ke suka faɗa satar mutane.

Ya kuma ce ya kamata a ƙarfafa hukumomin tsaro tare da ba su goyon bayan da ya dace don kawo karshen matsalar satar mutane.

Yanzu dokar ta'addancin da aka yi kwaskwarima ta 2021, bayan tsallake karatu na biyu, an gabatar da ita ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan wanda zai mika wa Kwamitin Kula da Harkokin Shari'a da ƴan cin Dan Adam don ci gaba da yin nazari.

An kuma ba Kwamitin makwanni hudu ya gabatar da rahotonsa ga Majalisar

Wannan layi ne

Kusan a kullum masu garkuwa da mutane na ci gaba da satar jama'a domin neman a biya su miliyoyin kudi kafin su sake su, a wasu lokutan kuma sukan kashe su ko da an biya kudin.

Ra'ayoyin mahukunta sun sha bamban game da yin sulhu ko kuma bayar da kudin fansa ga ƴan bindiga da ke garkuwa da mutane

Daya daga cikin masu adawa da biyan kudin fansa ga 'yan bindigar shi ne Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, wanda ke ganin bayar da kudin fansar daidai yake da karfafa gwiwar masu aikata wanna munnuna aiki.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle kuma na ganin sulhu da ƴan bindiga ne kawai zai kawo ƙarshen matsalar maimakon amfani da ƙarfi.