Matsalar Tsaro: Sojoji sun yi gargadi game da juyin mulki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta yi gargadi ga masu kira a gare ta domin ta kwaci mulki daga hannun gwamnatin farar hula da su kiyaye ta.
Rundunar ta yi gargadin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafinsu na intanet.
Ya ce sojoji ba za su sanya kansu cikin lamarin da zai gurgunta mulkin dimokradiyya ba, yana mai karawa da cewa za su murkushe duk wani yunkuri na kifar da gwamnati.
"An jawo hankalin manyan jam'an soji bisa kalamin da wani da ake kira Robert Clark SAN ya yi, inda yake bayar da shawara cewa jagororin mulkin siyasa su mika mulki ga sojoji domin sauya fasalin kasar nan. Rundunar sojin Najeriya tana mai tsame kanta daga wannan kalami da ya ci karo da tsarin dimokradiyya," in ji Birgediya Janar Nwachukwu.
Ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya tana "son yin amfani da wannan dama domin ta gargadi 'yan siyasar da ba su da alkibla wadanda ke son mulkin kasar nan ba ta hanyar zabe ba da su guji yin irin wannan tunani" domin a shirye sojoji suke su kare kasar.
"Muna son tuna wa dukkan jami'an soji cewa yin tunanin juyin mulki laifi ne na cin amanar kasa. Za a hukunta duk wanda aka samu ya hada baki wajen aiwatar da irin wannan shiri," a cewar Birgediya Janar Nwachukwu.
Kakakin rundunar sojin ta Najeriya ya ce matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar abubuwa ne da za a iya shawo kansu yana mai cewa suna hada gwiwa da sauran jami'an tsaro wajen magance su.
Rashin tsaron da ke addabar sassan Najeriya na ci gaba da jan hankalin 'yan kasar, musamman game da abin da suke gani sakaci ne na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shawo kansa.
Kasar na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a arewa maso gabas da arewa maso yamma, yayin da masu fafutikar ballewa daga Najeriya na kungiyar IPOB suke ci gaba da kai hare-hare kan 'yan sanda da wasu jami'an tsaron a kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.
A makon jiya, fitaccen malamin addinin Kirsitan ne wanda a baya ya goyi bayan Shugaba Buhari, Rabaran Fada Ejke Mbaka, ya yi kira ga shugaban kasar ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi.
Ya ce shugaban kasar ya gaza kare rayukan jama'a don haka bai ga amfanin ci gaba da zamansa a kan mulki ba.












