Yadda Shugaban Kungiyar Kirista ya gina masallaci a Adamawa

Most Reverend Stephen Dami mamza
Bayanan hoto, Most Reverend Stephen Dami Mamza da wasu shugabannin Musulmai a lokacin bude masallaci

A wani abu da ba a saba gani ba a ƙasa irin Najeriya, wani malamin addinin kirista ya gina masallaci ga wasu 'yan gudun hijira mabiya addinin Musulunci domin gudanar da ibadarsu.

Faston na cocin katolika wanda shi ne shugaban ƙungiyar kiristocin Najeriya ta CAN a jihar Adamawa, Most Reverend Stephen Dami Mamza, ya ce ya gina masallacin ne don bai wa Musulmi a cikin 'yan gudun hijirar damar yin addininsu ba tare da tsangwama ba.

Ku latsa alamar lasifikar da ke ƙasa domin sauraron cikakken rahoton Salihu Adamu Usman.

Bayanan sautiRahoton Salihu Adamu Usman