GSSS Ikara: Jami'an tsaro sun murƙushe yunƙurin sace ɗaliban sakandare 307 a Kaduna

Daliban makarantar Ikara

Asalin hoton, @KDSG_MISHA

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Kaduna ta ce ƴan bindiga sun sake kai hari wata makarantar sakandaren Ikara inda suka yi yunƙurin sace ɗaliban makarantar.

Kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa ya ce ƴan bindigar sun abka makarantar sakandaren Kimiya GSSS Ikara ne da tsakar daren Asabar zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ya ce daliban ne suka sanar da jami'an tsaro lokacin da ƴan bindigar suka shigo makarantar.

"Nan take jami'an tsaron da suka hada da sojoji da ƴan sanda da ƴan sa-kai suka ruga makarantar tare da yin artabu da yan bindigar, suka kore su," in ji shi.

Ya ce,"an ceto dalibai 307 ba tare da sun samu wani rauni ba" a harin da sojoji suka murƙushe.

Gwamnatin Kaduna ta ce babu ɗalibin da aka ɗauka daga makarantar.

Sanarwar ta ce sojoji da ƴan sanda sun bi sawun ƴan bindigar bayan sun kore su.

An murƙushe yunkurin kai hari gidajen ma'aikata

Sanarwar ta ce kuma ƴan bindiga sun yi yunkurin kai hari rukunin gidajen manyan ma'aikata kusa da filin jirgin saman Kaduna kusa da ƙauyen Ifira cikin ƙaramar hukumar Igabi.

"An daƙile yunƙurin harin yayin da sojojin ƙasa da na sama suka yi musayar wuta da ƴan bindigar, kuma ƴan bindigar da dama sun tsere da raunin harsashen bindiga a jikinsu."

Hare-haren na zuwa bayan da ƴan bindigar da suka sace ɗaliban kwalejin harkokin noma ta jihar Kaduna a ranar Alhamis suka fitar da wasu hotunan bidiyo, da ke nuna ɗaliban suna roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sha bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yi wa 'yan fashin dajin afuwa ba, yayin da jihohi maƙwabta ke cewa sun ga amfanin sulhu da su.

Kuma sanarwar da gwamnatin ta fitar ba ta ce komi ba game da bidiyon ɗaliban na kwalejin harkokin noma da suke roƙon a ceto su.

Sai dai a sanarwar da ma'aikatar tsaro da lamurran cikin gida ta fitar ta ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da ganin ɗaliban da aka sace sun dawo lafiya ba tare da wani abu ya same su ba.

Satar ɗalibai domin kuɗin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya.

Tun watan Disamba, sama da ɗalibai 600 aka sace daga makarantu a arewa maso yammacin Najeriya, wanda ke nuna wani mummunan al'amari mai matukar tayar da hankali a matsalar satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Karo na huɗu kenan cikin mako biyu da ake shiga makaranta domin satar ɗalibai bayan ɗaliban kwalejin noma a jihar Kaduna da har yanzu suna hannun ƴan bindiga da kuma ɗaliban da aka ceto na makarantar sakandare mata a garin Jangebe a jihar Zamfara da ɗaliban makarantar Kagara a jihar Neja.