'Yan bindigar da suka sace ɗaliban Kaduna sun nemi miliyoyin kuɗin fansa

'Yan bindigar da suka sace ɗaliban kwalejin harkokin noma ta jihar Kaduna sun fitar da wasu hotunan bidiyo, da ke nuna ɗaliban suna roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su.

'Yan bindigar sun kai hari kwalejin mai suna Federal College of Forestry Mechanisation ce da ke Afaka a Ƙaramar Hukumar Igabi da misalin ƙarfe 11:00 na daren Alhamis kuma suka yi awon gaba da mutum 39, 23 mata da kuma maza 16.

'Yan fashin sun yi amfani ne da shafukan ɗaliban wajen wallafa bidiyon a Facebook. A ɗaya daga cikin bidiyon, ana iya ganin yadda ake dukan ɗaliban mazansu da matansu da tsabga a wani wuri da ya yi kama da tsakiyar daji.

"Waɗannan mutanen sun kewaye mu kuma sun ce za su kashe mu idan wani ya yi ƙoƙarin zuwa ceton mu," in ji ɗaya daga cikin ɗaliban wanda ya yi magana da harshen Ingilishi.

Ya ƙara da cewa: "Sun yi mana duka har sun ji mana raunuka sosai. Wasu daga cikinmu na kuka saboda raunukan da suka ji. Idan gwamnati ba ta zo ta kuɓutar da mu da wuri ba, muna cikin gagarumar matsala."

Wata mace da ta yi magana da Hausa ta bayyana cewa "'mutanen nan sun faɗa mana cewa idan sojoji suka yi yunƙurin cetonmu, ko ɗaya daga cikinmu ba wanda zai koma gida".

A wani bidiyon, ana iya jin ɗalibai mata da ke zaune a bayan mazan suna cewa "ku ba su kuɗin fansar kawai. su sake mu don Allah" cikin Hausa da Ingilishi.

Wasu daga cikin iyayen ɗaliban da BBC ta tattauna da su sun ce 'yan bindigar sun buƙaci naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sha bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yi wa 'yan fashin dajin afuwa ba, yayin da jihohi maƙota ke cewa sun ga amfanin sulhu da su.

Sai dai, ita ma gwamnatin tarayya ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewa ba za ta shiga maganar sulhu da 'yan fashin daji ba.

An ceto wasu daga hannun 'yan bindigar - Gwamnatin Kaduna

Tun farko, wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojoji sun yi nasarar kuɓutar da ɗalibai da yawa kafin 'yan bindigar su gudu da su.

"Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130.

Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba", in ji Aruwan.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.

A jihar Kaduna kaɗai, 'yan bindiga sun kashe mutum 937 sannan suka yi garkuwa da 1,972 a shekarar 2020.

Sanarwar ta kuma cewa dakarun soji ne suka kai dauki cikin makarantar, inda suka fafata da 'yan bindigar.

Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun samu raunuka, kuma ana duba lafiyarsu a wani asibitiin sojoji na Kaduna, a cewar sanarwar.