An yi jana’izar sojin Najeriya bakwai da suka mutu a hadarin jirgin sama

Asalin hoton, Other
An yi jana'izar jami'an sojin saman Najeriya bakwai da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin sama da ya auku ranar Lahadi, tare da binne su a makabartar kasa da ke unguwar Lugbe kan hanyar zuwa filin saukar jiragen sama na Abuja, a bisa tsarin soji.
Sojojin sun mutu ne bayan da jirgin da suke ciki mai kirar Beechcraft King Air B350i ya yi hadari a kauyen Bassa kusa da filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sakamakon lalacewar injin jirgin.
Ministan tsaro, Manjo Janar Salihi Magashi (mai ritaya), da babban hafsan tsaro Mano Janar Lucky Irabor, da babban hafsan sojin kasa Ibrahim Atahiru, da kuma babban hafsan sojin sama Air Vice Marshal Isiaka Amao da kuma iyalan mamatan ne suka halarci jana'izar don yin girmamawar karshe.

Asalin hoton, Nigerian Air Force
Sojojin da suka mutu su ne: Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Kyaftin), Flight Lieutenant Henry Piyo (Matukin jirgin), Flying Officer Micheal Okpara (Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Warrant Officer Bassey Etim Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Sergeant Ugochukwu Oluka (Masanin yadda jirgin sama yake tashi (ATOS), Aircraftman Adewale Johnson (Jami'in jirgin sama).

Asalin hoton, Other

Asalin hoton, Other

Asalin hoton, Other
Labarai masu alaka:







