Cryptocurrency: Shugaban CBN ya fusata matasa kan batun kuɗin intanet

Bicoin

Asalin hoton, Bicoin

Lokacin karatu: Minti 3

Masu amfani da shafukan sada zumunta musamman matasa a Najeriya sun harzuƙa sakamakon kalaman da shugaban Babban Bankin ƙasar CBN, Godwin Emefiele, ya yi cewa ba za su taɓa amicewa da kuɗin intanet na cryptocurrency ba.

Mr Emefiele, wanda ya bayyana a gaban majalisar dokokin tarayyar ƙasar ranar Laraba, ya ce kuɗin na intanet ba abu ne da ake yi sanya ido a kansa ba don haka ba za su amince a yi mu'amala da shi a ƙasar a matsayin kuɗi ba.

A cewarsa: "Ina so na tunawa kowa cewa batun cryptocurrency wanda shi ne abin da ya haɗa mu a wannan rana, ana bayyana shi a matsayin kuɗin intanet wanda ba a san galibin waɗanda suke mu'amala da shi ba, kuma ba za a iya sanya ido a kansu ba, inda suke amfani da wasu alƙaluman lissafi da ke ɓoye yadda suke mu'amala ga masu hulɗa da su da kuma masu sanya musu ido. Don haka za mu iya cewa kuɗin intanet gaibu ne."

Ya ce "mutanen ɓoye ne" suke hulɗa da kuɗin intanet waɗanda suke lulluɓe harkokin mu'amalar kuɗi."

Sai dai waɗannan kalamai sun fusata masu amfani da shafin Twitter inda suka yi wa shugaban babban bankin na Najeriya dirar mikiya.

Da yake martani kan kalaman, wani da ya bayyana kansa da suna Benue Giant, ya ce za a iya cewa bayanin da "shugaban CBN Godwin Emefiele kan cryptocurrency su ne raha mafi girma da aka yi a 2021."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi kuwa Oluomo cewa ya yi abin takaici ne kalamin shugaban CBN cewa ba za su amince da kuɗin intanet ba a yayin da bankunan manyan ƙasashe irin su Amurka, Birtaniya da Sweden suka sha alwashin yin mu'amala da masu kuɗin na intanet.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

A nasa ɓangaren, Mr Rouvafe, ya ce Najeriya tana da damar yin mu'amala da kuɗin intanet na cryptocurrency amma maimakon hakan Mr Emefiele da sauran masu ruwa da tsaki sun gwammace su jira sai dukkan ƙasashe sun yi gaba sun bar ƙasar a wannan harkar sanna su yi fargar-jaji.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Waiwaye

A farkon watan nan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan ƙasar da su rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kuɗin intanet na cryptocurrency, matakin da bai yi wa dubban 'yan ƙasar daɗi ba.

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ga bankunan hada-hadar kuɗi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kuɗi ba (NBFI) da kuma sauran ma'aikatun harkokin kuɗi.

"Ƙari a kan umarnin da aka bayar tun a baya, bankin (CBN) yana tunatar da ma'aikatun da ke mu'amala da kuɗaɗen intanet ko kuma dillalansu cewa haramun ne," a cewar sanarwar.

A shekarar 2017, CBN ya ce kuɗaɗen intanet irin su bitcoin da litecoin da sauransu ana amfani da su ne wurin ɗaukar nauyin ta'addanci da kuma halasta kuɗin haramun, ganin cewa ba a iya bin sawunsu.

"Saboda haka, an umarci dukkanin NBFIs da NBFIs da OFIs da su tantance mutanen da ke amfani da irin waɗannan kuɗaɗe sannan su rufe asusun ajiyarsu," a cewar umarnin.

Kazalika a 2018, CBN ya ce kuɗaɗen ba sa cikin abubuwan da mai su zai iya kai ƙara kotu idan yana neman haƙƙinsa a Najeriya.

Kasuwanci da kuɗin intanet

Miliyoyin mutane a faɗin duniya na amfani da manhajoji iri-iri da ke ba su damar yin kasuwanci ta intanet ba tare da ɗaukar ruwan kuɗi ba ko kuma tura kuɗin da suka ajiye a asusun ajiyarsu na banki.

Sukan sayi abubuwan amfani daga wasu kamfanoni da suka amince a biya su da kuɗin intanet, kuma suna biyan kuɗin ne ta asusun wayar hannu ta salula.

Akwai manyan attajiran duniya da ke amfani da kuɗin intanet irin Elon Musk, wanda shi ne mafi arziki a duniya a yanzu.

A farkon watan Fabarairun nan ne attajirin ya ce "Bitcoin abu ne mai kyau" har ma ya yi nadamar rashin fara amfani da shi tun shekara takwas da suka gabata.

Wannan yabo da Musk ya yi wa kuɗin ce ta sa darajar Bitcoin ta kai dala 34,500 kafin daga bisani ta ragu. A watan Janairu, darajar tasa ta kai har dala 38,000 bayan Musk ya sauya sunansa zuwa #bitcoin a shafinsa na Twitter.