Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsangayar Asali: Yadda fim kan asalin almajirci ya ja hankalin Gwamnan Kano Ganduje
Gidauniyar KDC da kungiyar Motion Pictures Production sun hada gwiwa da gwamntin Jihar Kano da ke Najeriya wajen kaddamar da wani fim kan almajirci.
Fim din mai suna Tsangayar Asali an shirya shi ne domin yin waiwaye kan asalin almajirci a arewacin Najeriya da kuma irin tasirinsa ga rayuwar al'ummar yankin, a cewar daraktansa Hassan Giggs.
Ya kara da cewa wani abin ban sha'awa shi ne yadda fim din yake nuni da irin sauye-sauyen da suka kamata a yi wajen inganta almajirci.
Tsangayar Asali, wanda aka kaddamar da shi a wurin wani biki da aka yi a fadar gwamnatin jihar Kano, yana fadakarwa kan yadda za a gina wa almajirai azuzuwa da sanya tsarin boko a cikin manhajarsu da kuma bayar da kudin makaranta kamar yadda ake yi a tsarin makarantun boko.
Hassan Giggs ya ce hakan zai sa almajirai su samu nutsuwa wajen koyon karatun Alkur'ani ba tare da sun rika fita yawon barace-barace ba.
Manyan masu ruwa da tsaki ne suka halarci wurin kaddamar da fim din na Tsangayar Asali cikinsu har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakinsa Nasiru Gawuna, Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero da kuma malaman addini.
Jaruman da suka fito a fim din sun hada da Hadizan Saima, Malam Inuwa, Abdul U. Zada, Nura Sharu da Baba Sadiq.