Sheikh Abbduljabbar: Gwamnatin Kano za ta shirya muƙabala tsakanin malamin da sauran malamai

Asalin hoton, KNSG
Gwamnan Jihar Kano ya amince da shirya muƙabala ko kuma tattaunawar ilimi tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malamai a jihar biyo bayan zargin malamin da yin kalaman da suka saɓa wa Musulunci.
Matakin ya biyo bayan wata ganawa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi ce da malaman ƙungiyoyin addini na jihar, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abba Anwar, ya fitar ranar Lahadi ta bayyana.
Sanawar ta ƙara da cewa nan gaba kaɗan gwamnati za ta saka rana da kuma wurin aiwatar da muƙabalar, wadda malamai daga wajen Jihar Kano za su halarta.
Gwamna Ganduje ya yarda a gudanar da taron muƙabalar ne biyo bayan kiran da Abduljabbar ya yi na cewa a yi masa adalci, a cewar sanarwar.
Yadda za a gudanar da muƙabalar

Asalin hoton, Mujamma'u Ashabulkahfi Warraqeem Kebbi State
"An bai wa waɗanda za su fafata a muhawarar mako biyu domin su tattara bayanai da maudu'an da za su tattauna a kai," a cewar gwamnatin Kano.
Waɗanda suka halarci taron da Gwamna Ganduje sun haɗa da malamai daga ƙungiyoin addini da Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhammad Tahar Adam da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano da tsohon ɗan takarar gwamna, Malam Salihu Sagir Takai.
Bayan kammala taron ne kuma Ganduje ya amince a shirya muƙabalar.
An amince cewa dukkanin ƙungiyoyin addini za su turo wakilansu yayin muƙabalar, sannan za a gayyaci wasu manyan malamai daga wajen Kano domin su shaida.
Kazalika, Gwamna Ganduje ya yarda a yaɗa muhawarar kai-tsaye a gidajen rediyo na jihar da na ƙasashen waje.
Gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankali a lokaci da kuma bayan muƙabalar.
Abin da ya sa muka hana Abduljabbar yin wa'azi - Gwamnatin Kano

Asalin hoton, KNSG
A ranar Alhamis da ta gabata ce gwamnatin Kano ta amince da haramta wa fitaccen malamin yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar nan take.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammadu Garba ne ya tabbatar da hakan ga BBC.
Ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar na ranar Laraba bayan wasu rahotanni da ke nuna cewa malamin na yin kalaman da ka iya haifar da fitina a jihar.
''Gwamnati ta tsaya ta yi nazari, kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, har akwai rahotanni daga wajen manyan malamai da kuma hukumomin tsaro, dalilin da ya sa jami'an tsaro suka sanya kwamiti na musamman don duba irin waɗannan kamalamai da malamin ke yi'' a cewarsa.
Ya ce sakamakon tattaunawa a kan wannan batu da majalisar zartarwar jihar Kanon ta yi ne yasa ta amince da cewa, ba shakka kalaman nasa na iya haifar da tarzoma, don haka ta bada umarnin hana shi yin wa'azi a ko ina a faɗin jihar.
Matakan da aka ɗauka a kan Sheikh Abduljabbar sun haɗar da rufe masallacinsa dake unguwar Filin Mushe, da kuma hana shi yin wa'azi ko huɗuba a ko ina fadin Kano.
Kazalika an shawarce shi ya guji yin kalaman tashin hankali a ko ina ciki har da kafafen sada zumunta da ake yaɗa wa'azinsa, har zuwa lokacin da hukumomi za su kammala bincike.
Gwamnati ta buƙaci kafafen watsa labarai a jihar su kauce wa sanya wa'azinsa, tana mai cewa yin hakan ma na iya haifar da tashin hankali a cewarsa.
Gwamnati ta zalunce ni - Sheikh Abduljabbar
Shehin malamin ya bayyana dakatarwar da gwamanatin Jihar Kano ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".
Shiekh Abduljabbar ya faɗa wa BBC cewa duk da ita gwamnati da kanta, ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar, ta tabbatar da abin da ake yi masa zalunci ne, amma ta dakatar da shi ba tare da ba shi damar kare kansa ba.
Abduljabbar dai na waannan kalami ne biyo bayan rufe makarantarsa da masallacinsa da gwamantin Kano ta sanar da yi a ranar Laraba tare da haramta saka karatunsa a kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai a jihar.
Shehin malamin ya ce taron da ya gudanar a makon da ya gabata na daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin, ganin cewar duk yunƙurin hana taron ya ci tura.







