Somaliya : Yadda mayaƙan Al-Shabab suka kai hari otal a Mogadishu

Mogadishu

Asalin hoton, Getty Images

Masu kaifin kishin Islama a Somaliya sun kwashe tsawon awanni suna artabu da jami'an tsaro a wani otal a Mogadishu, babban birnin ƙasar.

Ƙungiyar Al-Shabab ta ce ita ce ta kai harin a otal din na Afrik, kuma ta ce ta kashe mutane da dama ko da yake har yanzu hukumomi basu sanar da adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

Su dai jami'an tsaro a nasu ɓangaren sun ce an ceto mutane da dama daga otal ɗin.

Kungiyar Al-Shabbab wacce ke da alaka da ƙungiyar al-Qaeda, ta jima tana kai hare-hare a kai a kai kan gine-ginen gwamnati da kuma farar hula ƴan ba ruwana.

Tunda farko dai wata mota ce ta danna kofar shiga otal din kuma ta tashi kafin, daga bisani maharan suka kutsa cikin otal ɗin, a cewar jami'ai da wasu da ke wurin.

"Fashewar ta sanya otal din girgiza, mun kaɗu matuƙa yayin da muke zaune a ciki muna tattaunawa. Mun firgita, mun rude," kamar yadda wani dake wajen lokacin da lamarin ya faru ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mogadishu

Asalin hoton, Reuters

Mayaƙan sun kai hari Otal ɗin na Afrik ne duk da cewa yana cikin wuraren da suka fi tsaro sosai kusa da babban filin jirgin saman birnin, a cewar wakiliyar BBC Bella Hassan wadda a halin yanzu ke can.

Otal din sananne ne wurin taruwar jami'an gwamnatin Somaliya ne, kuma wani kyaftin din 'yan sanda na yankin ya ce wasu' yan majalisa da manyan jami'an soji suna ciki a lokacin da aka kai harin.

Hotuna da aka nuna a shafukan sada zumunta sun nuna baƙin hayaƙi na tashi a duk fadin garin a safiyar ranar Lahadi.

Lamarin na faruwa ne ƴan makonni bayan da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin a janye wasu dakaru 700 wadanda suka kasance suna tallafawa ƙoƙarin rundunar tsaron cikin gida kan kungiyoyin' yan bindiga, ciki har da al-Shabab.

Ana fargabar ficewar na iya haifar da karin rashin zaman lafiya a ƙasar, wadda ya kamata ta gudanar da zabe a watan gobe.