Burtaniya ta yi amai ta lashe kan tayin bai wa masu korona £500 don su zauna a gida

Woman in masks walk along a street in London on 21 January 2021

Asalin hoton, Getty Images

Ofishin Firayim Ministan Burtaniya ya ce babu shirin bai wa ko wane dan Burtaniya £500 da ya kamu da korona don ya zauna a gida.

Mai magana da yawun Boris Johnson ya ce dama can akwai wannan tsarin a kasa ga masu karamin karfi wadanda ba za su iya aiki daga gida ba idan suka kamu da cutar korona.

Wasu bayanan sirri da suka fita daga Hukumar Lafiya ta Kasar sun nuna cewa an yi shawarar biyan ko wane dan Burtaniya mai dauke da cutar korona fam 500.

Akwai fargabar cewa wannan taimakon kudin ba zai yiwu ba saboda ma'aikatan da ake biya albashi mara yawa ba za su yarda su killace kansu ba.

Amma wani babban jami'i ya kawo shakku kan wannan shawara, yana cewa wasu jami'ai ne suka nemi a rika bayar da wannan kudi, amma Firaiministan yayi watsi da hakan.

Kaddamar da wannan shiri na bayar da fan 500 zai iya lakume fan miliyan 453 a mako guda - zai ninka kudin da kasar ke biya sau 12.

Wakiliyar BBC Katie Razzall ta ce minista ya san cewa killace kai domin dakile korona ba karamin abu ba ne, kuma wannan shawara masu kula da walwalar ma'aikata ce da Hukumar Lafiya ta kasar suka gabatar da shi.

Ta ce nan ba da jimawa ba kwamitin da ke yaki da korona wanda Micheal Gove ke jagoranta zai tattauna batun, tana mai cewa wasu mutane da yawa ba sa tsayawa a gida idan an umarce su don haka akwai bukatar daukar matakin gaggawa.

Woman in mask walks past Covid information sign in London

Asalin hoton, Getty Images

Jaridar Guardian ce ta fara wallafa wannan labari.

Amma Wakilin BBC na bangaren siyasa Ben Wright ya ce abu ne mai wuya a ce za a fara aiwatar da wannan tsari a ko wannne lokacin, lokacin da ake tsaka da fama da koma baya a baitil malin kasar.

Ya kuma ce maganar bayar da wasu 'yan canji don tausar mutane su zauna a gida magana ce da ake tattauanawa a gwamnatance.

A watan Satumbar da ya gabata ne aka mayar da shi doka ga duk wanda aka tabbatar yana da korona ya killace kansa.

Amma fam 500 da za a rika bayarwa, za a rika bayar da su ne kawai ga mutanen da ke da karancin albashi wadanda ba za su iya aiki daga gida ba.

Irin kuma kudin da za a rika bayarwa kenan a Scotland da Wales idan mutum ya cika wadannan sharudda. Northern Ireland za ta bai wa 'yan kasarta kyautar kudi, iya yadda ta ga dama, don biyan bukatunsu na yau da kullum kamar su cefane.

Akwai wasu sharudda na musamman da sai mai neman kudin ya cika kan a ba shi, amma wadanda ba su cancanci hakan ba da wadanda albashinsu ba shi da yawa ko kuma wadanda suke fuskantar rashin kudi saboda killace kansu da suka yi za su iya neman kudin tallafi daga gwamnati.

Amma an samu gaggarumin adadin mutanen da suka ki amincewa kan wannan kudin tallafin a Ingila, kididdigar da kungiyar 'yan kwadago ta tattara BBC kuma ta ruwaito.

Tsakanin watan Oktoba da Disambar shekarar da ta kare, kashi daya cikin uku na 49,877 da suka nemi wannan kudi an yi watsi na bukatarsu, kamar yadda bayanan suka nuna.

Sakataren harkokin cikin gida George Eustice ya shaida wa BBC cewa ana bibiyar shirin ba da tallafin ga mutanen da suka killace kansu.

Ya ce ba karamin kalubale ba ne killace kai musamman ga mutanen da basu da wata hanyar samun kudin da ta kamata don haka suna da bukatar ci gaba da aiki.

"Dole mu duba duka wasu tsare-tsare da za su iya sanya mutane su bi dokokin da aka sanya, idan za su iya bi to za mu iya ganin adadin masu kamuwa na raguwa," in ji shi.