Gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Sokoto 'ta laƙume miliyoyin naira'

Gobara

Asalin hoton, Sokoto government

Lokacin karatu: Minti 2

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira.

Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne da safiyar yau Talata kuma zuwa lokacin wannan rahoto, wutar na ci gaba da ci.

A hukumance, ba a san musababbin tashin gobarar ba, sai dai bayanai sun ce gobarar ta soma tashi ne daga Kofar Yan Roba.

Jami'an hukumar kashe gobara sun gargzaya kasuwar inda suka yi ta kokarin kashe wutar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Naru Bello, wani dan kasuwa ne da ke da shago a kasuwar, ya shaida wa BBC cewa gobarar ta tashi da misalin karfe bakwai na safe kuma ta cinye dukkan kayan da ke shagonsa da ma na wasu abokan sana'arsa.

Ya ce masu kashe gobarar sun fuskanci kalubale saboda yadda aka gina shaguna a kan hanya.

Shi ma Zaiyanu Yahaya Assada, wanda daya ne daga cikin 'yan kasuwar, ya ce gobarar ta kona kusan daukacin kayansa yana mai cewa barayi suna shiga suna sata.

Shugaban gudanarwa a babbar kasuwar ta birnin Sokoto, Alhaji Ibrahim mil Goma, ya ce 'yan kasuwar ne da kansu suka lalata hanyoyin da ke ciki kasuwar shi ya sa masu aikin kashe gobara suke shan wahala wurin kashe ta.

A cewarsa, gwamnati ta yi bakin kokarinta wajen gyara kasuwar.

Gwamnan jihar ta Sokoto, Aminu Waziri tambuwal, wanda ya ziyarci kasuwar, ya kuma jajanta wa 'yan kasuwar ta Sokoto Central Market bisa wannan ibtila'i.

Tambuwa

Asalin hoton, Sokoto government