An gano inda na'urorin bayanai suke na jirgin da ya yi hatsari

Asalin hoton, GM FIKRI IZZUDIN NOOR
An gano inda na'urorin naɗar bayanai suke na jirgin fasinjan nan da ya afka cikin teku bayan tashinsa a Jakarta, babban birnin Indonesia, ranar Asabar, a cewar hukumomi.
Wasu ƙananan jiragen ruwa ne suka shiga aikin neman jirgin da kuma sojojin ruwa masu ninƙaya da zummar gano na'urorin.
Tuni aka gano tarkacen jirgin da kuma wasu sassan jikin mutane.

Asalin hoton, EPA
Jirgin na Sriwijaya Air Boeing 737 na ɗauke da mutum 62 a lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa a kan hanyarsa ta zuwa Borneo daga Jakarta.
"Mun gano inda na'urorin na black box suke, duka biyun," in ji Soerjanto Tjahjono, shugaban kwamitin kiyaye haɗurra na Indonesia.
"Masu ninƙaya za su fara nemansu kuma muna sa ran ba za a ɗauki wani lokaci ba wurin ɗauko su."
Shafin da ke bin diddigin jiragen sama Flightradar24.com ya ce jirgin ya yi tafiyar mita 3,000 (ƙafa 10,000) cikin ƙasa da minti ɗaya yayin da yake gangarowa ƙasa.
Jirgin ba ƙirar 737 Max ba ne, jirgin kamfanin Boeing wanda ya sha yin hatsari a cikin 'yan kwanakin nan.
Wakilin BBC na Kudancin Asiya Jonathan Head ya ce tekuna a Indonesia ba su fiya zurfi ba sosai kuma rashin kyawun yanayin da ya riƙa kawo tsaiko wurin neman jirgin yanzu ya inganta.











