Gwamna Ganduje da ma'aikatan shari'a sun ja layi kan yankan albashi

Ma'aikatan gwamnatin jihar Kano na neman sanya kafar wando daya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa zarge-zargen zabtare musu albashi da suka ce gwamnatin na yi.

Kungiyar ma'aikatan fannin shari'a ta jihar Kano, JASU ta shigar da kara tana neman kotu ta taka wa Gwamna Ganduje burki kan datse musu albashi da gwamnatinsa ke yi.

A cewar shugaban kungiyar ma'aikatan kungiyar, Mukhtar Rabi'u Baba " mu ba mu san dalilin da ya sa gwamnati ta yanke mana albashi ba a watannin Nuwamba da Disamba kuma mun ga alamar tana so ta ci sake yanka a watan nan na Janairu. Wannan ne ya sa muka garzaya kotu domin a dakatar da gwamnatin."

Tuni dai wata babbar kotu a jihar ta wadda mai shari'a Usman Na'abba ke jagoranta ta nemi Gwamna Ganduje da ya dakata da yanke albashin ma'aikatan sannan ta dage karar zuwa ranar 28 ga watan Janairun nan.

To sai dai gwamnatin ta ce yanke albashin ma'aikatan na dan wani lokaci ne kuma karancin kudaden shiga ne suka sa ta aiwatar da hakan.

Kwamishinan Shari'a na jihar ta Kano, Barista Musa Lawal ya ce " mu a shirye muke mu bi duk hukuncin da kotu ta yanke. Kuma mun zauna da kungiyar Kwadago kafin mu fara yanke albashin inda muka sanar da su cewa za mu yanke na dan wani lokaci kasancewar yadda gwamnatin tarayya ke yankewa jihohi kudadensu."

To sai dai kungiyar Kwadago ta bakin shugabanta na kasa, Kwamared Ayuba Wabba ya ce sam ba su san zancen ba.

"Kungiyar Kwadago ce ta sa hannu a yarjejeniya da gwamnatin jihar Kano? Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba saboda Gwamna Ganduje bai aiwatar da albashi mafi karanci na naira 30,000, ka ga kenan ba za mu taba jituwa da shi ballantana har mu cimma wata yarjejeniya."

Korafe-korafen yanke albashin dai na zuwa a dai-dai lokacin da ma'aikatan jihar suka shiga sabuwar shekara da shaukin ci gaba da karbar sabon tsarin albashi mafi karanci na naira 30,000.

Gwamnatin jihar ta Kano dai ta fara biyan albashin mafi karanci amma kuma sai daga baya take neman komawa gidan jiya wato biyan ma'aikatanta albashi da tsohon tsari na naira 18,000.

Awatan Yulin 2019 ne dai shugaba Muhamamdu Buhari ya amince da biyan albashi mafi kankanta na naira 30,000.

To sai dai tun a lokacin wasu jihohi suka furta cewa sabon tsarin ya fi karfinsu sakamakon rashin karfin aljihu da suke fama da shi.