Katin ɗan ƙasa: Abin da ya sa Pantami ya dakatar da wasu ma'aikatan NIMC

Asalin hoton, Pantami Twitter
Ministan sadarwa na Najeriya Dakta Isa Ali Pantami ya bayar da umarnin dakatar da wasu jami'an hukumar samar da rijistar ƴan ƙasa NIMC, da ake zargi da karɓar wasu kudade daga hannun mutane kafin su yi musu rijistar a ofisoshinsu na Bauchi da kuma Kaduna.
A baya-bayan nan ne dai hukumar ta bayyana ɗaukar matakai masu tsauri kan duk jami'an da aka kama da yin zagon kasa ga shirin yi wa 'yan kasar rijista, a yayin da 'al'umma ke ruguguwar ganin cewa sun yi samu shaidar zama ƴan ƙasar.
Ministan ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya jaddada ɗaukar matakai masu tsauri kan duk jami'in da aka kama da karɓar cin hanci da rashawa a yayin gudanar da aikin rijistar shaidar zama ɗan kasa, da ya ce tamkar yin zagon ƙasa ne.
A cikin shekarar da ta gabata ne Dr Isa Ali Pantami ya bayar da umarnin cewa ƴan Najeriyar su tabbatar sun sada lambobin wayarsu ta salula da kuma ta shaidar zama ɗan kasar, wanda kuma sai wanda ya riga ya yi rijistar ɗan ƙasar ne zai iya samun wannan lambar.
Wannan mataki in ji sanarwar ya biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe daga jama'a a jihohin Bauchi da Kaduna, a kan cewa wasu daga cikin jami'an hukumar NIMC, na karɓar na goro kafin su yi wa mutane rijistar, wacce tuni hukumomi suka riga suka bayyana cewa kyauta ce.
Dole ne in ji wannan sanarwa, sai duk jami'an da aka ɗora wa alhakin gudanar da aikin yi wa ƴan Najeriyar rijistar shaidar zama ɗan ƙasar sun nuna dattaku da sanin ya kamata muddin ana so a samu nasarar cimma burin da ake buƙata.
Mutane da dama a kasar na ta tururuwa zuwa cibiyoyin da aka tanada domin yin wannan rijista a faɗin Najeriyar, inda galibi ke kokawa da tsananin cunkoso da jinkiri wajen yin gudanar da aikin domin samun lambar.
Ruguguwar dai ta biyo bayan umarni da kuma wa'adin da hukumomin da suka bayar cewa duk wanda bai samu ya yi rijistar da kuma sada lambar shaidar zama ɗan kasar da wayoyin salularsa ba, za a rufe duka layukan nasa.

Asalin hoton, Twitter
Hukumar dai ta ƙara yin kira ga ƴan Najeriyar da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen bayar da tasu gudumawar, ganin cewa aikin rijistar ɗan kasar ya gudana cikin nasara ta hanyar kwarmata bayanai kan duk wanda ya nemi su bayar da cin hanci kafin a yi musu rijistar a cibiyoyi daban-daban a fadin kasar.
Da ma dai a wata hira da BBC a makon jiya, daraktan hukumar NIMC Injiya Aliyu Aziz Abubakar, ya jaddada hakan ga 'yan kasar domin tauna tsakuwa aya ta ji tsoro.
Ko shakka babu irin wannan dabi'a in ji wasu yan Najeriyar za ta iya sanya gwiwar masu aniyar zuwa don a yi musu rijistar, idan aka duba halin da jama'a ke ciki na neman abin rufin asiri, duk kuwa da cewa babu wanda zai so ya ga an toshe masa layukan wayoyin salularsa idan bai sada lambar shaidar zama dan kasar da su ba kamar yadda hukumomin suka umarta.
A ranar 19 ga watan Fabrairu ne dai NIMC ta ce wa'adin da aka ɗebar wa ƴan Najeriyar na yin rijistar zai ƙare, a yayin da kuma ranar 19 ga wannan wata na Janairu shi ne wa'adin da aka ɗebar wa waɗanda suka riga suka yi rijistar ya zamana sun laƙana lambobinsu da na wayoyin salularsu.












