An kama matashi da zargin yanke al'aurar yarinya ƙarama a Jihar Bauchi

Rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ce ta yi nasarar kama matashi da zargin yanke wa wata yarinya mai shekara shida wani ɓangare na al'aurarta.

Kakakin 'yan sandan jihar Ahmed Mohammed Wakil, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

"A ranar Laraba 30 ga Disamba muka samu rahoton cewa an ga wata yarinya cikin jini, abin da ya sa jami'anmu suka ruga da ita zuwa Babban Asibiti na Jama'are kuma likita ya ce an yanke wani ɓangare na al'aurarta da wani abu mai kaifi," a cewarsa.

"Bayan gudanar da bincike ne kuma aka kama wani mai suna Adamu Abdul Ra'uf ɗan shekara 20 a Gandu, inda ya ce ya haɗa kai da wani mai suna Abdulkadir Wada Haladu wurin aikata laifin."

DSP Mohammed Wakil ya ce ya zuwa yanzu Abdulkadir ya tsere amma suna "dukkanin bakin ƙoƙarinsu domin ganin sun kama shi cikin hanzari" sannan kuma suna ci gaba da bincike.

Kwamishinan "Yan Sandan Bauchi CP Lawan Tanko Jimeta ya bayar da umarnin a mayar da lamarin hannun sashen binciken manyan laifuka "domin kyakkyawan bincike".

A gefe guda kuma, rundunar ta kama wasu matasa guda huɗu da take zargi da kafa ƙungiyar aikata fashi da makami.

Binciken da rundunar ta gudanar ya zargi matasan da kafa ƙungiyar mai suna "Bager",

Ya ce sun kama wani ɗan shekara 18 mai suna Idris Yakubu ranar Alhamis yayin da yake yunƙurin aikata fashi a gidan Alhaji Garba Bello da ke garin Bauchi ɗauke da bindiga ƙirar gida.

"Bayanan da ya bayar sun kai mu ga kama Umar Abdullahi mai shekara 19, da Hassan Lawal mai 18, da Sadik Ilyas mai 18, waɗanda bincike ya nuna 'yan ƙungiyar Bager ne," in jni sanarwar.

Ya ƙara da cewa an ƙwace bindiga ƙirar gida a hannunsu tare da ƙunshin harsashi guda biyu.

Sanawar ta yi kira ga mazauna Bauchi da su ci gaba da bai wa rundunar bayanai da zummar daƙile aikata miyagun laifuka a jihar.