Tsattsauran ra'ayin Musulunci a Faransa: Majalisar ministocin ƙasar ta goyi bayan dokar kawar da kaifin kishin Islama

Majalisar ministocin Faransa ta amince da ƙudurin dokar da ke neman daƙile tsattsauran ra'ayin Musulunci bayan jerin hare-haren da masu tsattsauran ra'ayin suka kai a kwanan baya.

Daftarin dokar, wani ɓangare ne na ƙoƙarin da Shugaba Emmanuel Macron ke yi na dogon lokaci, domin ganin an tabbatar da ƙasar a matsayin ƴar ba-ruwana da kowanne addini, ta hanyar tsaurara dokoki kan makarantun gida da kalaman nuna ƙiyayya.

Wasu masu suka a Faransa da ƙasashen waje, sun zargi gwamnatinsa da amfani da dokar domin auka wa addini.

Sai dai Firaiministan Faransa Jean Castex ya kira ta "dokar kariya" wacce za ta ƴantar da Musulmai daga ƙangin masu tsattsauran ra'ayi.

Ya dage kan cewa ba wai an samar da dokar ne domin ta shafi wani addini ba musamman musulunci.

Me dokar ke cewa ?

Ƙudirin dokar "mai goyan bayan ka'idojin Jamhuriyya" zai tsaurara matakan taƙaita kalaman nuna ƙiyayya ta hanyar intanet da kuma hana amfani da intanet domin bayyana bayanan sirri game da wasu mutane.

Ana ganin wannan a matsayin martani ga fille kan malami Samuel Paty a watan Oktoba.

Wani mai tsattsauran ra'ayi ne ya kashe Paty, mai shekaru 47, bayan ya nuna wa ɗalibansa zanen barkwanci na Annabi Muhammad (SAW).

Dokar ta kuma haramta makarantun "sirri" waɗanda ke yaɗa aƙidar Islama tare da tsaurara dokoki kan karatun gida.

Haka nan za ta ƙarfafa dokar hana auren mata fiye da ɗaya ta hanyar ƙin bayar da izinin zama ga masu neman auren mata da yawa.

Za a iya cin tara ko haramta wa likitoci yin gwajin budurci ga 'yan mata.

Akwai sabbin ƙa'idoji game da mu'amala da kuɗi ga ƙungiyoyin musulmai da kuma buƙatar su sanya hannu kan ƙa'idojin Jamhuriyyar Faransa domin samun kuɗaɗe.

An tsawaita dokar hana jami'ai sanya tufafin addini a wurin aiki ga ma'aikatan sufuri da ma'aikata a wuraren ninƙaya da kasuwanni.

Me yasa aka gabatar da dokar?

An ɗauki tsawon lokaci ana nazarin wannan daftarin dokar, amma hare-haren masu kaifin kishin Islama na baya-bayan nan ya sake ƙarfafa buƙatar samar da ita.

Kisan Paty na daga cikin hare-hare uku da suka fusata Faransa.

An kashe mutane uku ta hanyar daɓa musu wuƙa a a cocin Nice a watan Oktoba.

An caka wa ƙarin wasu mutane biyu wuƙa da ji musu mummunan rauni a watan Satumba a Paris kusa da tsohon ofishin mujallar Charlie Hebdo, inda masu kaifin kishin Islama suka kai mummunan hari a 2015.

Shugaba Macron ya kasance mai kishin kare martabar Jamhuriyyar Faransa ciki har da matsayin kasar a ƴar ba ruwana da kowanne addini.

Ya bayyana addinin Islama a matsayin ''addinin rikici'' kuma ya kare ƴancin jaridar Charlie Hebdo na buga zane-zanen Annabi Mohammed.

Faransa tana da kimanin Musulmai miliyan biyar.

Wanne martani ake mayarwa ?

Mutane da dama a faɗin duniya musamman a ƙsashen musulmai na yi wa Mista Macron kakkausar suka a ƙasashe da dama da ke da rinjayen Musulmai.

Dangantakar ƙasarsa da Turkiyya, wacce tuni ta yi tsami, ta ƙara taɓarɓarewa inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana dokar a zaman "tsokana ce ta buɗe ido" kuma ya ce Mista Macron "yana da taɓin hankali".

An gudanar da zanga-zanga a Pakistan da Bangladesh da Lebanon.

Wakilin Amurka kan ƴancin addini, Sam Brownback, shi ma ya yi suka, yana mai cewa: "Lokacin da kuka sami ƙarfin iko, lamarin na iya kara taɓarɓarewa."

A Faransa ita kanta, wasu 'yan siyasa masu sassaucin ra'ayi sun nuna damuwa kan yadda da alama dokar na iya tozarta musulmai.

Jaridar Le Monde ta ce hakan na iya shafar sauran ƙungiyoyin addini da ke koyar da karatu a cikin gida.

Amma wakiliyar BBC a Paris Lucy Williamson ta ce matsin lamba ya ƙara ƙamari kan lallai Shugaba Macron da ya ɗauki mataki.