Bazoum Mohammed: Yadda kotu ta wanke shi kan takardun shaidar zama ɗan ƙasa na bogi

A Jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da mai da martani a kan hukuncin kotun tsarin mulkin ƙasar da ya wanke ɗan takarar jam'iyar PNDS Tarayya, Bazoum Mohamed.

Wani ɗan takarar shugabancin Nijar, Abdulkadri Alfa, ta bakin lauyansa, ya ce har yanzu ba su gamsu da hukuncin kotun ba.

Lauyan mai shigar ƙara ya ce a bisa ƙa'ida dai ba a ƙalubalantar hukuncin kotun ƙoli amma ba wai don ba zai iya taɓuwa ba ne.

Lauyan ya ce har yanzu basu gamsu da takardun kariyar da Bazoum Mohammed ya gabatarwa kotu ba inda ya ce ko shakka babu za su sake shigar da ƙara kan takardun.

To amma a bisa tsarin dokoki ƙasar, hukuncin kotun ƙoli baya tashi don haka ake ganin da wannan hukuncin an kawo ƙarshen mujadala a kace-nacen da ake kan takardar zama ɗan ƙasar Bazoum Mohammed ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyya mai mulkin ƙasar.

Tun kafin yanke wannan hukunci dai an yi yaɗa jita-jitar cewa kotu ta kori takarar Bazoum Mohammed.

Yadda Bazoum da magoya bayansa suka ji bayan yanke hukunci

Idrissa Waziri, shi ne mai magana da yawun Bazoum Mohammed, ya ce sun yiwa Allah (SWA) godiya, da ya gwada musu cewa an kawo ƙarshen duk wani ce-ce-kuce.

Ya ce, a yanzu kotun ƙoli ta yi watsi da zargin da ake yiwa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya inda aka ce shi ba cikakken ɗan ƙasa bane.

Idrissa Waziri ya ce: "Kowa ya san cewa ɗan takararmu cikakken ɗan ƙasa ne da ya shafe shekara fiye da talatin yana siyasa ba kuma a san shi da aikata wani aikin ashsha ba".

Irin ayyukan da ya yi a ko ina ana yabawa dashi ba shida wata matsala da za ace yau gashi an same shi da ita inji mai magana da yawun Bazoum Mohammed.

Waiwaye

An dai kwashe tsawon lokaci ana ta cacar-baka tsakanin masu son ganin an soke takarar Bazoum Mohammed bisa zargin da suke cewa shi ba ɗan ƙasa bane da kuma masu kare shi.

To amma a yanzu komai yazo ƙarshe kasancewar kotun ƙolin ƙasar ta wanke shi daga zargin cewa shi ba ɗan ƙasa bane.