Shin da gaske ana shirin mayar da Najeriya kasar Musulunci?

A cikin wasiƙun da 'yan jaridar Afrika ke turo wa BBC, Mannir Ɗan Ali, wanda shi ne Tsohon Editan Jaridar Daily Trust, ya yi dubi kan ce-ce-ku-cen da aka yi kan haruffan Larabcin da ke jikin takardun kuɗin Najeriya da kuma tambarin sojojin ƙasar.

Wani lauya ne ya buƙaci kotu a jihar Legas da ke Najeriya da ta umarci babban bankin Najeriya ya cire haruffan Larabci wanda aka fi sani da rubutun Ajami da ke jikin kuɗin ƙasar.

Haka kuma yana buƙatar a cire rubutun Larabcin da ke jikin tambarin rundunar sojojin Najeriya inda aka rubutua "Nasara daga Allah".

Sai dai mutane da dama ba su san cewa haruffan Larabci da ake amfani da su a wurin rubutun sauran harsuna ba ana kiran rubutun "Ajami".

Wannan ce hanya ta farko da aka fara karatu da rubutu a nahiyar, ɗaruruwan shekaru kafin zuwan Turawan mulkin mallaka da kuma Kiristocin Mishan da suka zo da rubutun Turanci.

Ba Hausa kaɗai ba, harsuna kamar irin su Swahili da ke Gabashin Afrika da Tamashek da kuma harsunan Tuareg da ke Arewacin Afrika da Yammacin Afrika, da kuma harsunan Najeriya kamar Kanuri da Yarabawa da Fulani da Nupe duka suna amfani da Ajami.

Manyan malamai da kuma ma'aikatan gudanarwa ta Daular Usmaniyya wadda ta mamaye arewacin Najeriya a ƙarni na 19, duk sun yi amfani da rubutun Ajami domin rubuta littafai da dama.

Nana Asma'u, wadda 'ya ce ga Shehu Usmanu Ɗan Fodio, ta shahara wurin rubutun waƙoƙin zube - kuma da yiwuwar ita ce mace ta farko da ta fara amfani da rubutun Ajami domin rubuta littafai da yawa na Hausa da Fulatanci.

Sama da shekara 150 bayan mutuwarta, rubutun Ajami na Hausa ne ba wai Larabaci ba ne ke jikin kuɗin Najeriya ba.

Rikicin Addini

Rabuwar kai mai tsanani da kuma rashin yarda na daga cikin manyan matsalolin Najeriya tun bayan da Turawan mulkin mallaka suka haɗe arewa da kudancin Najeriya, da kuma yankin Legas a 1914.

Har yanzu, wasu daga cikin 'yan siyasar ƙasar na kallon wannan mataki a matsayin "kuskuren da aka yi a 1914".

Rabuwar kan da aka samu ta jiɓanci ta al'adu da addini da kuma fahimtar mutane waɗanda aka gama kansu wuri guda a matsayin ƙasa ɗaya.

Duk da cewa kafafen watsa labarai suna kwatanta cewa "akasarin arewacin Najeriya Musulmai ne da kuma akasarin 'yan kudanci Kiristoci ne" wanda hakan ba lallai ya nuna asalin girman baban-babancen Najeriya ba, hakan ya fito da matsala ɗaya ce kacal.

Wannan matashiyar ta yi bayani kan yadda wannan ce-ce-ku-cen da ke gaban kotu a Legas a yanzu ya samo asali.

An fara irin wannan musayar yawun ne kusan shekara 10, a lokacin da ake murnar cika Najeriya shekara 50 da samun 'yancin kai, sai aka sauya fasalin naira 50. Bayan shekara huɗu, ita kanta naira 100 sai da aka yi mata kwaskwarima.

Hakan ya jawo babban ce-ce-ku-ce a tsakanin Musulmai da Kiristocin ƙasar bayan an yi amfani da rubutun Turanci wajen rubuta adadin kuɗi da Hausa maimakon Ajami.

Wani rubutu da aka yi a Mujallar New Yorker ya taƙaita batun da cewa: "Wasu Kiristoci na goyon bayan wannan mataki a matsayin wani yunƙuri na cire Najeriya daga turbar Musuluntar da ƙasar, inda akasarin Musulman ƙasar na ɗaukar hakan a matsayin ƙin jinin Musulunci".

A bayyane take kan cewa waɗanda suke adawa da amfani da haruffan Larabci a kuɗaɗen Najeriya na kallon rubutun Ajami a matsayin Musulunci inda suke kwatanta asalin Ajami da Larabci sakamakon Larabci harshe ne na Musulmai, inda suke ganin asalin abin da yasa ake amfani da Ajami shi ne a yaɗa Musulunci a faɗin Nahiyar Afrika.

Sun kasa gane cewa sun fara irin tunani irin na 'yan Boko Haram, inda masu iƙirarin jihadin da suka shafe kusan shekara 11 suna yaƙi a arewacin Najeriya suke sukar duk wani abu da ke da alaƙa da karatun boko.

Rubutun Ajami da aka yi a kowace takardar kuɗin Najeriya an yi shi ne domin miliyoyin Hausawa waɗanda rubtun Ajami kaɗai za su iya karantawa da rubutawa, wanda ake koyarwa a makarantu da ke faɗin arewacin ƙasar.

Irin waɗannan mutanen za su iya zuwa kotu domin ɗaukaka ƙara kan cewa an tauye musu haƙƙi idan aka cire rubutun Ajami.

A daidai lokacin da ake ci gaba da wannan muhawara ta rubutun Ajami a jikin kuɗin Najeriya, wasu a kafafen sada zumunta sun yi sauri sun nuna cewa akwai rubutun Larabci a jikin kuɗin Isra'ila, kuma an yi rubutun ne sakamakon Larabawa marasa rinjaye da ke zaune a ƙasar.

Tambarin sojojin Najeriya da gaske rubutun Larabci ne a kai kuma wani Kirista ɗan kudancin Najeriya ne ya yi tambarin, domin kawar da tunanin da ake yi na cewa tauraron da ke ƙarƙashin ungulun da ke kan tambarin na kama da na Yahudawa.

Kamar yadda wani ya mayar da martani ga Mujallar New Yorker kan sabon tsarin da aka yi wa kuɗin Najeriya na shekara 100, ya ce : "Idan aka bar rubutun Turanci kuma ba neman mayar da mutane Kiristoci ake yi ba, me ya sa na Larabci ne kawai ake cewa neman Musulantar wa ne?

Ko ma wane hukunci kotu za ta yanke, da alama hukuncin ba zai zama ƙarshen wannan batu ba.