EndSars: A yi amfani da hanyoyin da hukuma ta tanada don dawo da doka da oda - Buhari

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaro umarnin yin amfani da duk hanyoyin da hukuma ta tanada don dawo da doka da oda a wuraren da rikici ya ƙi lafawa.

Shugaban ƙasar ya faɗi hakan ne a yayin taron Kwamitin Tsaro da aka gudanar a fadarsa a yau Alhamis, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin da suka shafi kafofin sada zumunta Bashir Ahmad, ya wallafa a Tuwita.

''Zuciya cike da damuwa da baƙin ciki da takaici kan abubuwan da suka faru a cikin sa'a 48 da suka gabata, muna fatan kar mu sake ganin irin wannan masifar,'' kamar yadda saƙon na Bashir ya bayyana.

Saƙon ya kuma ce shugaban ƙasar ya bai wa dukkannin hukumomin tsaro umarnin yin amfani da duk hanyoyin da hukuma ta tanada don dawo da doka da oda a wuraren da lamarin ya shafa.

Haka kuma shugaban zai yi wa ƴan ƙasar jawabi da misalin ƙarfe bakwai na yammacin yau, don sanar da muhimman matakan da zai ɗauka wajen kawo ƙarshen zanga-zangar EndSars a faɗin ƙasar.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Munguno ne ya sanar da hakan bayan kammala taron kwamitin tsaron.

Mahalarta taron Kwamitin Tsaron na yau sun haɗa da shugaban ƙasar da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ma'aikatan Fadar shugaban ƙasa da shugabannin rundunonin soji da Sufeto Janar na ƴan sanda da kuma shugabannin sauran hukumomin tsaro.

Majalisar na da ikon bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro, kamar yadda Kundin Tsari ya ba su dama.

Taron na zuwa ne bayan da aka shafe ƴan kwanaki ana zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa rikici a wasu sassan Najeriya.