Zanga-zangar #EndSars ta tilasta rufe makarantu a Legas

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Legas ta rufe makarantu a faɗin jihar sakamakon tashin hankali da zanga-zangar EndSars da ke ci gaba da gudana a wasu biranen Najeriya ke haifarwa.

Ma'aikatar Ilimin jihar ta ce ƙare daliban shi ne abu mai muhimmanci, sannan an bukaci iyaye su sa ido kan inda yaransu ke shiga a wannan yanayi da ake ciki.

An samu tashe-tashen hankula a birane da dama na Nijeriya yayin da zanga-zangar nuna adawa da zaluncin 'ƴan sanda da ke ci gaba da gudana haifarwa.

Legas ta bada wannan umarni ne biyo bayan rikice-rikice da ke sake ruruwa a faɗin jihar, inda akwai rahotannin rufe manyan hanyoyi da ke haddasa cunkoson ababen hawa.

Iyayen yara sun shaida cewa wannan yanayi ne marar daɗi da suka tsinci kan su.

Wani Uba da BBC ta tattauna da shi ya ce babban tashin hankalinsa shi ne yadda ake ganin makamai da bindigogi a inda ake zanga-zangar.

Sannan sun ce suna farin ciki da matakin gwamnati domin zai kare rayukan 'ƴa'ƴansu.

Wannan yanayi da aka shiga na zuwa ne bayan zaman kullen korona na tsawon watannin da ya hana dalibai daukar darasi ko zuwa makaranta saboda annobar korona.

Yanzu haka dai an bada umarnin ci gaba da karatu ta intanet da sauran kafofin da aka yi amfani da su lokacin kullen korona zuwa lokacin da lamura za su dai-daita.

Zanga-zangar EndSars dai na ci gaba da tada hankali, baya ga Legas an samu tarzoma a Abuja da Benin da kuma Kano.

Tsawon mako biyu masu zanga-zangar na fitowa kan titi musamman a Abuja da Legas ba fashi, duk da gwamnati ta ɗauki mataki tare da alƙawalin biyan buƙatunsu.