Coronavirus: Mutumin da ya kamu da cutar korona mai tsananin har sau biyu

Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga James Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Lafiya da Kimiyya

Wani mutum a Amurka ya kamu da cutar korona sau biyu, inda ta zo masa da tsanani a karo na biyun, a cewar rahoton likitoci.

Mutumin mai shekara 25 ya buƙaci taimakon asibiti bayan da huhunsa ya daina kai masa iskar da yake shaƙa cikin jikinsa.

A yanzu dai ya warke, kuma ba a faye yin cutar sau biyu ba sai ga mutane kaɗan.

Amma binciken mujallar Lancet ta cututtuka masu yaɗuwa ya dasa tambayoyi kan yawan garkuwar jikin da ake buƙata don yaƙi da cutar.

Mutumin, wanda ya fito daga yankin Nevada ba a san shi da wasu matsalolin lafiya ko rashin garkuwar jiki mai ƙarfi da za su sa ya kamu da Covid-19 ba.

Me ya faru a waɗannan ranakun

  • 25 ga watan Maris - Matakin farko na alamunta sun bayyana da suka haɗa da maƙaƙin maƙogwaro da tari da ciwon kai da tashin zuciya da gudawa
  • 18 ga Afrilu - Gwaji ya gano ya kamu da cutar a karon farko
  • 27 ga Afrilu - An magance alamomin farko
  • 9 da 26 ga watan Mayu - Gwajin da aka yi masa sau biyu a ranaku daban-daban sun nuna ya warke daga cutar
  • 28 ga Mayu - Ya sake nuna alamunta, wannan karon har da zazzaɓi da ciwon kai da jiri da tari da tashin zuciya da gudawa
  • 5 ga Yuni - Gwaji ya sake nuna ya kamu da cutar a karo na biyu, kuma hakan ya zo masa da ƙarancin iskar da yake shaƙa da ke shiga cikin jini da shan wahalar jan numfashi.

Masana kimiyya sun ce mutumin ya kamu da cutar koronan sau biyu ne, ba wai ƙwayar cutar da ta kama shi a karon farko ne ta sake dawowa ba.

Wani haɗin ƙwayoyin cutar na lokuta biyun da ya kamu da aka yi ya nuna cewa ya kamu da cutar ne a lokuta daban-daban ba ta farkon ce ta sake bijirowa ba.

''Bincikenmu ya gano cewa don mutum ya kamu da farko hakan ba zai kare shi daga sake kamuwa ba,'' a cewar Dr Mark Pandori, na Jami'ar Nevada.

Ya ce ko da mutanen da suka warke ya kamata su ci gaba da bin matakan kariya ne yin nesa-nesa da juna da sanya takunkumi da yawan wanke hannu.

Har yanzu masana kimiyya na ƙoƙarin gano wani lamari mai sarƙaƙaiya kan batun cutar korona da garkuwar jiki.

Shin kowa ne yake samun kariyar garkuwar jiki daga cutar? Ko da mutanen da alamun cutar ba sa bayyana sosai a jikinsu? Zuwa tsawon wane lokaci kariyar ke zama a jikinsu?

Akwai tambayoyi masu muhimmanci kan fahimtar yadda cutar za ta iya shafar mu a tsawon lokaci da kuma irin tasirin da za ta yi kan riga-kafi.

Zuwa yanzu, ba a faye samun masu sake kamuwa da cutar ba - misalan masu irin hakan ba shi da yawa daga cikin mutum miliyan 37 da suka kamu a duniya.

Rahotanni daga Hong Kong da Belgium da kuma Netherlands sun nuna cewa cutar ba ta sake tsanani kamar na farkon.

Sai dai a yayin da ƙasashe ke fuskantar zagaye na biyu na sake ta'azzarar cutar, to wataƙila za mu samu amsoshin tambayoyin.

Sai dai ana sa ran zagaye na biyu na cutar ba zai yi tsanani ba don tuni jiki ya koyi yadda zai yi yaƙi da ƙwayar a wannan karon.

An kasa gano dalilin da ya sa cutar ta fi tsanani a jikin Nevada a karo na biyu. Amma ana tunanin ko yawan ƙwayar cutar da ta shiga jikin nasa a karo na biyun ta fi yawa ne.

Farfesa Paul Hunter na Jami'ar East Anglia ya ce, akwai abin damuwa dangane da binciken saboda tazarar da ke tsakanin lokacin kamuwa da cutar sau biyu, da kuma tsananin da ta biyu ta yi.